Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Published: 3rd, October 2025 GMT
Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari.
Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro sai suka maida wannan daular ta zamo daular da ke shan jini, amma ainihi wani sarki ne daga cikn daular Usmaniyya, amma ba haka abin yake ba, kila walitta yake nuna masu, kila wani abu ya nuna masu. Muhimmin abin da nake son in fada idan a wannan fim din wannan shu’umi (actor) ya sha jini ko ya ba wani jininsa (to wannan jini na Dirakula shi ne Kudubi), su da shi ke ba su san Allah ba, shi ya sa suka kawo misali da jinin jikin mutane, to duk wanda mutumin da ya sha sai ya rika jin duk wani motsi da halittar Allah, haka nan da sauro zai kada fukafukansa a karshen duniya da zai ji a kunnensa, wannan kenan.
Turawa suka shirya, kar ka ga ba su da addini, kwarewa ko sani cikin wadannan abubuwa. A’a suna da shi, suna da addini da malamai suna da Falsafofi, suna da Ruhubanai da kullum suke a cikin halwa. Idan kana bin irin wadannan fina-finai za ka ga abubuwan mamaki.
Akwai wani fim da kasar Ingila ta shirya na ‘The Seeker”, Falillahi, idan za ka kawo misali koda waye ka kawo muddin za a fahimci ilimi, Allah zai iya buga misali da sauro ko gizo-gizo, kafirai suka ce kuma misali ya kare da ake buga misali da sauro. Allah ba ya jin kunyar buga msali da komai, don haka nan mu ma za mu kawo don mu fahimci ilimi ba mu tsoron buga misali da The Seeker da Merlin da sauransu.
Yanzu wannan The Seeker din, idan ka lura yadda suka shirya fim din, shi Kudubi ne mai zaman kansa, amma shi kansa bai san kansa ba, shi kuma yana da wasu masu kiyayeshi, yana da wani kudubi Zaitu wanda shi ya san waye wannan, shi ya san sigar nan, kuma kiyaye shi yana hannun Zaitun nan, Allah ya hada shi da wasu mata, akwai wata ta iya tarbiyyantarwa, akwai wata Sufiya da duk wasu Kuduai ba su da tasiri a kanta, wannan abu duk akwai shi. Shehu Tijjanin Abul Abass (RTA), ya ce yafi mafatihul Kunuzi ta wani wajen su kuma sun fi shi ta wani wajen.
Sayyidina Kabiru ya za ci ya san duk Waliyyan Allah, sai da ya je Baitul Mukaddasi ya ga Abdulrazaki mutane sun kewaye shi yana ba da karatu, sai ya ga wani yaro a kwance yana bacci, sai ya zo ya yatshi yaro ya ce kai ba ka jin kunya duk mutane suna wajen Abdulrazaki suna karatu, sai ya ce ka kyale ni malam, ni wajen Razzaku nake karatu, mu ba a wajen bawan Razzaku muke ba, a wajen Razzaku muke karatu, sai ya ce yi kwanciyarka, sai ya ga cewa akwai aiki a gabansa.
To a cikin wannan fim din, akwai wata kalma da Zaitu yake fada wa wata mata da yake tafiya da ita, ya ce ki duba yau mu ne muradin Allah a kan kasa, Allah mu yake kallo a kan kasa, mu Allah ke nufi a kan kasa amma kuma ko gida ba mu da shi a doran kasa a daji muke yawo, wannan ya nuna cewa ba wai don kana waliyi shi kenan kai dan mai da nono ne, kai sai kaza da kaza ba.
Yayin da yake tafiya da wannan yaro, duk da ya dame su, sai ya ce ke wannan yaro da kike gani shi ne duniya gaba daya, wani ruhi ne, idan wannan yaro ya rushe shikenan duniya ta kare, duniya fanko ce, wannan yaro shi ne duniya.
Ilimin walitakka, ba wani ilimi ne sabo da aka kago ba , ilimi ne da dama yana nan tun farko, duk malamai masu hikima masu halwa suna nan da shi, akwai wani matsayi da Waliyi yake hawa, ya na samu ne daga zikiri da halwa da tunani da abin da Allah ya rubuta masu suke kaiwa wannan matsayi, suna jin halittar Allah kaf da kunnensu kuma wannan ba ta kare masu jin wancan ba, ba ta shagaltar da shi wancan ba, kuma yana harkokinsa na rayuwa yana baccinsa yana aurensa, kaga wannan ya fi karfin hankali, wannan Kudubi ke da irin wannan.
Sayyadi Ali, Allah ya kara masa yarda, shi ke maganar walitta, shi ne asalin Sufaye gaba daya, sunansa waliyi waliyen muminai wata rana yana kan hanyarsa ta zuwa yakI sai ya zo shigewa ta wajen da Annabi Sulaiman ya shige watau wadil Namli, daji ne na tururuwai, Salmanul Farisi ya kalli dajin bakikirin sai tururuwai, sai ya ce tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci wadannan tururuwai kuma ya san adadinsu, sai Sayyadi Ali ya ce, zo in koya ma tasbihi baka iya tasbihi ba, ka ce tsarki ya tabbata ga Allah da Ya halicci wadannan tururuwai, amma wasu bayin Allah sun san adadinsu, ka gan ni nan, na san adadinsu, na san mata a cikinsu na san kuma san maza, haka nan kuma na san masu kwai na san marasa kwai.
Shehu Tijjani Abul Abassi, ya ce idan har Kudubi ya zama haka wanda shi kuma tsakaninsa da Annabi kamar yadda tururuwa take da tafiyar shaho a sama, shi Annabi shi shi ne kamar mai tafiyar shaho a sama (wato saurin tafiyar), shi kuma Kudubi shi yake daidai da tafiyar tururuwa a kasa (wajen yanayin sauri) haka nan ganinsa da na Annabi duk da wannan tsarki na Kudubi, to mun gode wa Allah, Manzon Allah (SAW) shi ne Annabin annabawa, malamin malamai.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: wannan yaro
এছাড়াও পড়ুন:
Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Gaskiya ba abu ne mai kyau ba, ka nema ta hanyar halal din ma ya aka kare da kudin yanzu, bale kuma ta hanyar haram. Tsabar son abin duniya ne da rashin tsoron Allah, aji tsoron Allah a nemi halal, a nemi kudi ta tsabtatacciyar hanya.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:
Wannan maudu’i ne mai matukar muhimmanci, saboda talauci da son zuciya ya yi wa mutane yawa. Idanun mutane sun rufe, ba sa tunanin ya dace ko bai dace ba. Burinsu kawai shi ne a ina za su samu kudin da za su kashe wutar gabansu, ko kuma su cika burinsu na rayuwa. Lallai kuskure ne babba, a ce mutum ya zama idanunsa sun rufe akan abin duniya, ba ya tsoron Allah akan abin da zai ciyar da iyalinsa. A yayin da mutum ke neman kudi ido rufe, ba ya tunanin lahira ko hakkin wani, ko sakamakon abin da zai same shi, burinsa kawai abin da zai samu. Allah ya sa mu fi karfin zuciyar mu, mu dage da neman halal, mu tsira da mutuncin mu da imanin mu.
Sunana Hauwa Abubakar Sarki:
Lokaci ne da Allah ya kaho mu idan ba kana da shi ba ba za a yi da kai ba. Shi ne dalilin da ya sa wasu mutane suka fada neman kudi ta kowani irin hanya. Abun da za a ce shi ne, mu yi hakuri mu zauna a inda Allah ya aje mu, domin kuwa ba kowa ne Allah ya rubuta yana daga cikin masu arziki ba. Talauci shi ne dalili na farko dake janyo hakan da kuma hangen abun hannun wani, ko nace abun da wani ya samu kai ma kace lallai sai ka samu, wanda hakan ba daidai bane. Mu kasance masu taimako kana mu tsaftace neman mu sai mu ga Allah ya albarkaci abun da zamu samu.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya rashin yadda da kaddara ce ke jawo haka, domin duk mutumin da ya yadda da kaddara ya san duk wani rabon na dukiya ba zai wuce shi ba don haka ba zai bi hanya mara kyau wajen neman kudi ba. Eh to, dalilan dake jawo hakan suna da yawa, to amma jahilci da rashin tsoron Allah, sune a gaba, domin sune suke jawo haka ga mafi yawan mutane. To hanyoyin dai guda biyu ne, na farko neman ilimin addini domin da shi ne za ka san halak da haramin za kuma ka kiyaye su, sai na biyun tsoron Allah, domin koda kana da ilimi sai kana da tsoron Allah za ka kiyaye halak da haramin.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
Taulauci da rashin aikin yi, ga tsadar rayuwa da kullum take karuwa, nauyi na yi wa al’umma yawa suna rasa mafita a rayuwarsu, shi yake haifar da hakan. Wasu kuma son zuciya ne. Kowa ya rika tuna cewa akwai mutuwa, wanda ya yi daidai ya sani, haka ma wanda bai yi ba ya sani.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:
Neman kudi ya dace, amma ta hanyar halal. Abin da yake kawo hakan talauci da aka jefa al’ummar wannan kasar. Babbar hanyar ita ce, mu ji tsoron Allah muna tuna cewa bawa ba zai taba wuce rabonsa ba. Shawarata a nan ita ce mu tuna cewa babu bawan da zai koma ga ubangijinsa ba tare da ya bar daidai da kwayar zarra na arzikinsa ba, don haka mu tsaya mu nemi halal dinmu domin mu zauna lafiya. Allah ya sa mu dace amin.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Gaskiya wasu talauce ne, wasu kuma san abu duniya ne ya yi masu yawa, shi ya sa suke neman kudi ta kowace hanya. Ni na ga wata da idona wanda har sai da nasa baki, amma na ga ta yi nisa ba ta jin kira. Wai za ta kasar waje neman kudi, babu inda ya fi gida dadi. Shawara ta a nan shi ne, in zamu nemi kudi mu neme shi ta hanya mai kyau, kuma mu kula. Allah ya ba mu dace wa.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori:
A yau, yawaitar matsin rayuwa da kalubalen yau da kullum ya sa mutane da dama ke neman kudi ba tare da la’akari da halal ko haram ba. Wani zai nemi hanyar kirki ya samu na halak, amma wasu kuma za su zabi hanyar da ba ta dace ba kamar sata, damfara, ko karuwanci, duka da nufin biyan bukatunsu na yau da kullum. Wannan hali yana da illa ga dabi’a, addini da tsaron al’umma. Idan kowa zai nemi kudi ta kowacce hanya, to rayuwar al’umma za ta zama barazana, domin ba za a samu gaskiya, aminci da mutunci ba. Mu fahimci cewa arziki na gaskiya yana zuwa ne da hakuri, tawakkali, da bin hanyoyi na gaskiya da halal. Duniya ba za ta kare da wahala ba, amma samun riba ta haram tana da sakamako mai muni a nan duniya da lahira.
Sunana Hussy Saniey, daga Katsina:
Rashin tawakkali shi ne linzamin da ke kai wasu mutanen ga aikata haka. Ya kamata a kodayaushe mutane su rika jin tsoron Allah tare da tunawa yana kallonsu a duk wani motsinsu, don haka su kiyaye jikinsu daga haram, domin duk jikin da aka gina da haram ba ya shiga aljanna. Mutane su jajirce a wurin neman halal, duk wanda ya tashi ya nema Allah zai sanya ma shi albarka a cikin neman, a guji cin dukiyar da ba ta da tsarki.
Sunana Nura Garba, Tsanyawa, A Jihar Kano:
Yana da alaka da sauyin zamani da al’umma suke son yin kitsan wance amma basu da gashin wance, ga kuma tarun bukatu marasa manufa, da yanzu sai ka ga mutum yana neman kudi ta kowace hanya don kawai ya sai mota irin ta wani. Abin da yake kawo haka shi ne, rayuwar karya da yin gasa da wasu ke yi, sai rashin godiya ta rufin asiri da cikakkiyar lafiyar da Allah ya bawa dan’adam. Hanyoyin magance hakan yadda da samu da rashin na Allah ne, kuma kowa rabonsa zai ci kafin ya bar duniya, don haka ya kamata al’umma su nemi halak ta halastacciyar hanya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA