Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Dauki Nauyin Aurar Da Mata 300 Kafin Azumi
Published: 10th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kebbi, ta kammala shirye-shiryen gudanar da daurin auren mata dari uku a karshen watan Fabrairun wannan shekara.
Da yake zantawa da manema labarai da yammacin Lahadi, shugaban babban kwamitin kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Suleiman Muhammad Argungu, ya bayyana cewa, nasarar daurin auren da aka yi a shekarar da ta gabata, wanda gidauniyar NANAS ta uwargidan Gwamnan, Hajiya Nafisa ta shirya, ya sanya gwamnatin ta sami kwarin gwiwar daukar nauyin aurar da wasu rukunin a wannan shekarar.
A cewar Shugaban kwamitin, za a aurar da mutane 600 marasa galihu ba tare da la’akari da addini, kabilanci da siyasa ba a tsarin gwamnati.
Ya ce, an kafa kwamitocin tantancewa a dukkan kananan hukumomi 21 domin zabar ma’auratan da suka cancanta bisa ka’idojin da aka gindaya wadanda suka hada da tabbacin ango yana da abin yi do daukar nauyin iyalansa, da kuma matsugunin da za su zauna.
Suleman Argungu, ya bayyana cewa, dukkan ma’auratan za a yi musu gwajin lafiya na tilas, ciki har da gwajin kwayar cutamai karya garkuwar jiki ta HIV, da kwayoyin halitta na Genotype.
Za a biya Naira 180,000 a matsayin sadaki ga kowace amarya, wanda ya kama jimillar Naira miliyan 54, tare da kayan daki, da suka katifa, gado da kuma kayan amfanin gida.
Daga Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Aurar Da Mata 300
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sandan Niger Sun Hada ‘Yan’uwa Mutanen 35 Da Aka Ceto Da Iyalansu
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta saki tare da hada wadanda aka yi garkuwa da su talatin da biyar tare da iyalansu.
Sun kunshi mata goma sha shida da yara goma sha tara daga Kagara, Tegina da Agwara, bayan sun shafe makonni a hannun ‘yan sanda da ke tsare da kuma kawar da hankalinsu daga barayin da ke Minna.
Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman ya bayyana haka a lokacin wani takaitaccen bayani da ya mikawa shugaban karamar hukumar gidan rediyon Ayuba Usman Katako a Minna.
Kwamishinan ‘yan sandan wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Adamu ya wakilta, ya bayyana cewa za’a sake haduwa da wadanda abin ya shafa da iyalansu domin sun kasance karkashin kulawar ‘yan sanda tare da tallafi da kulawar da suka dace daga gwamnatin jihar Neja.
A cewarsa, hakan ya fara ne a ranar 3 ga watan Yulin 2025 lokacin da aka samu labari daga wata majiya mai tushe da ke nuna cewa wadanda abin ya shafa na kaura daga Birnin-Gwari a jihar Kaduna zuwa wasu yankuna.
Jami’an ‘yan sanda sun yi kaca-kaca da rukunin farko na st Agwara a kokarin da suke na tsallakawa kogin zuwa wasu kauyukan New-Bussa na jihar Neja tare da ceto mata biyar da kananan yara shida.
A yayin da ake gudanar da tambayoyi, an bayyana cewa ‘yan bindigar na yin kaura daga Birnin-Gwari zuwa wasu unguwanni kuma rundunar ‘yan sandan da ke aiki a hanyar Mekujeri zuwa Tegina ta cafke kashi na biyu tare da mata hudu da kananan yara bakwai, yayin da kuma aka kama wani rukunin tare da direban da ya tafi da su.
Bincike ya nuna cewa direban, Yusuf Abdullahi na Birnin-Gwari ya je sansaninsu ne domin kai mutanen da abin ya shafa, kuma yana kan bincike don tabbatar da hadin gwiwarsa a ayyukansu.
Kwamishinan ‘yan sandan, Adamu Abdullahi Elleman, ya tabbatar da cewa tun da aka tsare wadanda abin ya shafa, an ba su wasu shawarwari da nasiha, da abinci da kuma kayan kwanciya.
Ya kara da cewa, bayan samun takardar izinin da ya kamata, ana mika wadanda abin ya shafa ga shugaban karamar hukumar da ‘yan uwansu tare da yin kira ga jama’a da su baiwa ‘yan sanda bayanan da suka dace a duk lokacin da aka lura da al’amura domin gaggauta shiga tsakani.
PR ALIYU LAWAL.