Da alama tallafin da matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba wadanda hare-haren jihar Binuwai ya raba da muhallansu na Naira biliyan daya ya bar baya da kura.

Kwana daya da bayar da tallafin, ’yan gudun hijirar sun fito suna zanga-zangar yunwa, amma kakakin hukumar bayar da agaji ta jihar (SEMA), Terna Ager, ya ce musu kudin ba na sayen abinci ba ne.

Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya

Aminiya ta rawaito yadda Sanata Remi a ranar Talata ta ziyarci jihar inda ta mika wa Gwamnan Jihar, Hyacinth Alia tallafin kudin, a madadin ’yan gudun hijirar.

To sai dai kwana daya bayan hakan, sai wasu daga cikin ’yan gudun hijirar suka fantsama a kan tituna suna zanga-zangar yunwa da zargin masu kula da sansanin da gallaza musu tun da suka tare a can.

Mutanen dai sun tare babbar hanyar Makurdi zuwa Lafiya suna rera wakoki irin su “Gida muke so mu koma,” “Yunwa ta dame mu” da kuma “Matanmu na rasa ’ya’yansu suna yin bari”.

Daya daga cikin matan mai suna Rebecca Awuse, ta shaida wa ’yan jarida cewa, “Yunwa ta ishe mu. Ba mu da abinci, ba muhalli, ba magani sannan ba kulawar lafiya. ’Ya’yanmu na mutuwa da yunwa. Mata da yawa sun yi bari saboda yanayin da suke ciki sannan a kasa muke kwana.

Sai dai da yake mayar da martini, Terna Ager, ya yi zargin cewa akwai wata boyayyar manufar siyasa a zanga-zangar.

A cewarsa, “Babu dalilin da zai sa su yi wannan zanga-zangar sam. Wadanda ke sansanin Yelwata wani lokacin sukan koma sansanin Makurdi an fi samun tallafin abinci a can.

“Tallafin da matar Shugaban Kasa ta bayar na sake tusgunar da su ne ba wain a sayen abinci a raba musu ba ne. Kuma hakan ma yana daukar lokaci.

“Na yi imanin suna zanga-zangar ce saboda suna tunanin za a debi kudin kawai a raba musu, amma ba haka ba ne dalili,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Binuwai Yelwata yan gudun hijirar a zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse.

Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta.

A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse.

Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da Bello Musa Gada, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Kazaure, sai  Barrister Mustapha Habu a matsayin Sakatari kuma Lauya mai ba da shawara.

Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa an zaɓi waɗannan mutane ne bisa cancanta, ƙwarewa da kuma nagartar halayensu, yana mai kira gare su da su yi kokarin sauke nauyin da aka dora musu.

Sakataren Gwamnatin Jihar  ya ce an riga an mika musu takardun naɗi kuma sun shirya tsaf don fara aiki nan take.

A nasa bangaren, Muhammad Fa’iz ya gode wa Gwamna bisa amincewar da ya nuna musu, tare da alƙawarin gudanar da aiki da ƙwazo da himma.

 

 

Usman Muhammad Zaria 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato
  • An Yanke Wa Mai Gadi Da Mai Dafa Abinci Hukuncin Kisa Kan Kashe Tsohon Kwamishina A Katsina
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
  • Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
  • Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa
  • Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa
  • Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
  • Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa