Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu
Published: 8th, October 2025 GMT
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata.
Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye suNnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba.
A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba.
A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya bayyana cewa duk da cewa an ɗauki Nnaji a jami’ar a shekarar 1981, bai kammala karatunsa ba kuma ba a ba shi takardar kammalawa ba.
Haka kuma, jaridar ta ƙara da cewa Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) ta tabbatar cewa takardar shaidar hidimar ƙasa da Nnaji ke nunawa ta bog ice a wajen hukumar, kuma ba za a iya tabbatar da sahihancinta ba.
A cikin sanarwarsa, Onanuga ya tabbatar da cewa Nnaji ya sauka daga mukamin minister kuma mamba a Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC).
Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin ministan kuma ya yi masa fatan alheri.
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus ɗin Geoffrey Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, sakamakon wasu zarge-zarge da ake yi masa.”
“Shugaba Tinubu ne ya naɗa Nnaji a watan Agustan 2023. Ya yi murabus yau ta hanyar rubuta wasiƙa yana gode wa Shugaban Ƙasa da ya ba shi damar yin wa ƙasa hidima.”
“Nnaji ya ce ya kasance wanda abokan ahamayyar siyasa ke yi wa bita-da-kulli.”
“Shugaba Tinubu ya gode masa bisa gudunmawar da ya bayar, kuma ya yi masa fatan alheri a duk inda ya dosa,” in ji sanarwar Onanuga.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Takardun bogi
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.
Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.
“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.
RN