Aminiya:
2025-11-08@11:12:21 GMT

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe

Published: 21st, September 2025 GMT

Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa.

Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu

Hatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare.

Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep sannan ta ci karo da babbar motar.

Sakamakon haka, direban bas ɗin, Ibrahim Makeri, tare da fasinjoji biyu; Adamu Isiya da Alhaji Shaibu sun rasu nan take.

Daga baya kuma wani daga cikin waɗanda suka ji rauni ya rasu, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa huɗu.

An kai gawarwakin da kuma waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gashuwa da ke Ƙaramar Hukumar Bade.

Likitoci suka tabbatar da mutuwar waɗanda suka rasu, sauran kuwa suna samun kulawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin mota waɗanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe

Cin zarafin da Babban Jami’an tsaro (CSO) na Gwamnan Yobe,  CSP Yakubu Zakari Deba ya yi ga wakilin Talabijin NTA da ke Damaturu, Babagana Kolo a harabar Majalisar Dokokin Yobe da ke Damaturu a ranar Alhamis ya tada ƙura.

Lamarin ya faru ne yayin da wasu ’yan jarida ke jiran a shigar da su cikin zauren domin su bayar da rahoto kan gabatar da kasafin kuɗin 2026 da Gwamna Mai Mala Buni ya yi a gaban Majalisar Dokokin.

An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC

Shaidu sun ce Babban Jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba, ya afka wa Kolo ya buge shi a fuska, lamarin da ya yi sanadiyyar raunuka a bakinsa da wasu ɓangarorin jikinsa.

An ruwaito cewa, lamarin ya kawo cikas ga yadda kafofin yaɗa labarai ke yaɗa labaran taron yayin da ‘yan jarida ke barazanar ƙauracewa gabatar da kasafin kuɗin.

Sai da Kwamishinan Yaɗa labarai, Alhaji Abdullahi Bego ya sa baki kafin ‘yan jaridar su ci gaba da ayyukansu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
  • An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
  • Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia
  • Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku a Kudancin Lebanon  
  • Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
  • Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe