Masar ta yi watsi da wasan sada zumunta da Zambia kan Isra’ilawa na horar da ‘yan wasan kasar
Published: 3rd, September 2025 GMT
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba.
Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta.
Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga karshen watan Disamba zuwa tsakiyar watan Janairu.
Zambiya sau da yawa tana fafatawa da kasashen Larabawa da na musulmi ba tare da yin la’akari da alakar hakan da Isra’ila ba, sai dai kuma jami’an Masar sun bayyana cewa basu da matsala da mai horar da ‘yan wasan Zambia ko mataimakinsa wadanda Isra’ilawa ne, amma sun ba da misali da yakin da ake yi a Gaza da kuma manyan laifukan da Isra’ila take tafkawa kan fararen hula da cewa abu ne mai sosa rai, wanda kuma wadannan abubuwa su ne manyan dalilai na soke gasar.
Ana ci gaba da bincike kan “Isra’ila” a fagen kwallon kafa, a baya-bayan nan lokacin da kungiyar masu horar da ‘yan wasa ta Italiya (AIAC) ta yi kira ga FIFA da UEFA da su dakatar da “Isra’ila” daga gasar kwallon kafa ta kasa da kasa, saboda yakin da ake yi a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian: Idan Ba A Hada Kai Ba, Munanan Manufofin Amurka Zasu Hada Har Da Kasar China September 2, 2025 Baqa’i: Tawagar Turai Sun Fara Amfani Da Tsoffin Takunkumai Kan Kasar Iran September 2, 2025 Majalisar Shawarar Musulunci Ta Yi Zaman Na Musamman Kan Shirin Tawagar Turai September 2, 2025 Batun Kwance Makaman Kungiyar Hizbullahi Kokarin Kunna Wutar Fada Ne A Kasar Lebanon September 2, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Zirin Gaza Cikin Sa’o’i 24 Kacal September 2, 2025 Aragchi Yayi Tir da Kissan Firaiministan Kasar Yemen Da Wasu Ministocinsa September 2, 2025 Fiye Da Mutane 1000 Ne Suka Rasa Rayukansu A Yammacin Sudan Saboda Zaizeyar Kasa September 2, 2025 MDD Tace Yara Kimani 660,000 Ne Aka Hanawa Karatu A Gaza September 2, 2025 Beljium Ta Ce Zata Amince Da Samuwar Falasdinu A Cikin Wannan Nan September 2, 2025 Venezuela Ta Karbi Sakon Tallafi daga Tehran Kan Barazanar Amurka September 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ilBagaei ya yi tir da samar da duk wata hulda da HKI sannan tana ganin yin haka yana dai-dai da taimaka mata ko halatta mata ayyukan ta’addancin da take aikatawa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Tasnem na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana fadar haka a yau Laraba, a taron mako-mako da ya saba a ma’aikatsa a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, Iran tana kira ga dukkan kasashen duniya musamman kasashen yankingabas ta tsakiya da su kauracewa Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ko ta ina.
Ya ce kasashen musulmi da dama, har ma da wasu wadandaba musulmi ba sun dade da katse dangantakarsu da haramtacciyar kasar, babu dangantakar diblomasiyya babu na kasuwanci da ita. Don haka wadanda suka rage su yi da gaggawa.
Jami’in diblomasiyyar ya yabawa kungiyoyi daban-daban a kasashen turai wadanda suke kamfen na kauracewa HKI da kuma yanke hulda da ita ko ta ina, da kuma dakatar da sayar mata makamai wadanda take kashe falasdinawa da su.
Don haka ,inji Bagaei, idan kasashen musulmi suka shiga cikin gayyar wadan dannan kasashe da suka kauracewa HKI, suka kuma aiwatar da kauracewar a kasa, to kuwa zamu ga nasar babba nan gaba da yardar All…
Daruruwan Falasdinawa ne suka yi shahada a birnin Gaza babban birnin yankin saboda hare-hare babu kakkautawa da take kaiwa kan mutanen birnin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci