Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Ce Har Yanzu Akwai Guraben Biyan Kujerar Hajji
Published: 28th, February 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.
Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.
Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da bukatar zuwa Hajji su tuntubi jami’an hukumar a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar ko su ziyarci hedikwatar hukumar dake kan titin Katsina, a cikin garin Kaduna.
Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa mutum dubu uku da dari hudu da sittin (3,460) ne suka biya kudin Hajji ta hannun hukumar.
Ya kuma kara da cewa kudin Hajji ya kama naira miliyan takwas da dubu dari hudu da hamsin da bakwai da dari shida da tamanin da biyar, da Kobo hamsin da tara (₦8,457,685.59).
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Ahmed Makama Hardawa, ya rasu.
Marigayin ya rasu ne ranar Talata a Abuja, bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Muna tafe da karin bayani…