Jagora: Iran Tana Fuskantar Makiya Na Waje Kafirar Da Munafikai
Published: 3rd, March 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya.
Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan, da kuma lokacin da ya kamata a yi Magana da su, ko kuma lokacin da ya kamata a zare musu takobi.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karatun alkur’ani mai girma, a jiya Lahadi da dare, ya yi ishara da cutukan ruhi da su ka addabi bil’adama a wannan zamanin da su ka hada hassada, rowa,mummunan zato, ganda da son kai, da kuma fifita manufa ta kashin kai akan ta al’umma, tare da bayyana cewa, a cikin alkur’ani mai girma da akwai magungunan dukkanin wadannan cutukan.
Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce, a bisa mahanga ta musulunci abu na biyu mai muhimmanci bayan tauhidi da ilimi da kyautata alaka da Allah, shi ne shimfida adalci a cikin al’ummar musulmi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin Bayanai Kan Fashe-Fashe Wasu Abubuwa A Tashar Jiragen Ruwan Kasar Iran
Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya).
AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba.
Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.”
Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya ce: An cimma wasu bincike na farko dangane da yiyuwar yin sakaci a wannan fanni, kuma ana gudanar da bincike sosai kan dukkan al’amuran da suka faru. Kuma babu wata daga kafa da za a yi ga duk wanda aka samu da yin sakaci a kan haka za a tuhume shi kamar yadda shari’a ta tanada.
Ya ci gaba da cewa, “Ta hanyar nazarin faifan bidiyo daban-daban na aukuwar lamarin tashar jirgin ruwa ta Shahid Raja’i, an lura da cewa, an yi jigilar kaya a lokacin da lamarin ya faru, inda hayaki ke tashi, sai kuma fashewar wani abu.