Masar ta yi Allawadai da ikirarin Netanyahu game shirinsa na kafa Isra’ila Babba
Published: 14th, August 2025 GMT
Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba.
Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar da hankulan Larabawa kuma suka yi watsi da shi.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce “tana tabbatar da aniyarta ta abbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tare da yin Allah wadai da abin da wasu kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito dangane da abin da ake kira Isra’ila Babba.
Ya yi bayanin cewa, “ya bukaci a yi karin haske kan hakan, bisa la’akari da yadda lamarin ke nuni da alamun tada zaune tsaye, da kin amincewa da zaman lafiya a yankin, da kuma dagewa kan ta’azzarar rikici.”
Sanarwar ta jaddada cewa, wannan lamari ya ci karo da muradun sassan yanki da na kasa da kasa masu son zaman lafiya da ke son cimma daidaiti ta fuskar tsaro da zaman lafiya ga daukacin al’ummomin yankin.
Ya jaddada cewa “babu wata hanya ta samun zaman lafiya sai ta hanyar komawa kan teburin shawarwari, kawo karshen yakin Gaza, da kafa kasar Falasdinu.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas ta aike da wasikar yabo ga Yemen kan goyon bayan Gaza August 14, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Iraki Ta Mayar Da Martani Game Da Korafin Amurka Kan Yarjeniyar Tsaro da Iran August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa.
Ya rasu yana da sama da shekaru 100 a duniya.
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’aniBaya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba.
Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa.
Ga wasu daga ciki:
Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda yake da ’ya’ya da jikoki da tataba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani mai girma Kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, ya ba shi shaidar girmamawa saboda yawan zuri’a mahaddata Yana da ’ya’ya 95 Yana da jikoki 406 Yana da tattaba-kunne 100 ’Ya’yansa mahaddata Alkur’ani 77 Jikokinsa mahaddata Alkur’ani 199 Tattaba-kunnensa mahaddata Alkur’ani 12 Shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da fatawa a addinin Musulunci a Najeriya An haife shi a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira A ranar Laraba aka haife shi a a garin Nafada da ke Jihar Gombe a yanzu Kwararre ne a fannin Alkur’ani da Tafsiri da Ma’arifa da Hadisi da Harshen Larabci da Li’irabi da Fikihu Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi Digirin girmamawa Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR Ya musuluntar da dubban mutane Yakan yi saukar Alkur’ani duk bayan kwana biyu Mutane fiye da 140,924 suka haddace Alkur’ani a makarantunsa da ke fadin Najeriya Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,500 a Najeriya da wasu kasashen Afirka Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya Ya shafe shekaru sama da 50 yana gabatar da tafsirin Alkur’ani a cikin watan Ramadan