Leadership News Hausa:
2025-07-26@17:29:22 GMT
NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu
Published: 5th, February 2025 GMT
Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025.
Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan lokaci.Nijeriya Na Iya Fuskantar Ƙarancin Maniyyata A Hajjin Bana EFCC Ta Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar ₦144m A Gombe Farfesa Usman ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da ya gudana a manhajar ‘Zoom’ a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, 2025, tare da masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji. Shugaban Hukumar NAHCON ya yi kira ga Sakatarorin Zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha da su yi aiki tare da Hukumar don ganin an mika kudaden a kan lokaci, wanda ke da muhimmanci wajen tabbatar da biyan kudin masaukan da aka riga aka bincika kuma aka tanada.
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Masana kiwon lafiya sun bayyana yadda ruma ke yada matsalolin rashin lafiya ga lafiyar jikin mutum.
Musamman a lokuta irin na damina, ruma kan dabaibaye gidajen mutane da dama na tsawon lokaci wanda ka iya jawo matsaloli daban-daban ga lafiya da kuma gidajenmu.
NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makarantaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin matsalolin da ruma ke haifarwa ga lafiyar jikin namu.
Domin sauke shirin, latsa nan