Leadership News Hausa:
2025-11-08@15:42:53 GMT

Majalisar Dattawa Ta Buɗe Ofishin Sanata Natasha

Published: 23rd, September 2025 GMT

Majalisar Dattawa Ta Buɗe Ofishin Sanata Natasha

Yanzu da aka buɗe ofishinta kafin komawar zaman majalisar, hankali ya karkata kan zaman majalisar na watan Oktoba, don ganin ko za a gabatar da kuɗirin dawowarta, da kuma ko za a tilasta mata ta nemi afuwa kafin ta dawo ta zauna a kujerarta a cikin zauren majalisar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.

Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Dakatarwa Majalisar Dattawa

এছাড়াও পড়ুন:

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’.

 

Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA

A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai.

A babban aikinsu na farko, ’yan bindiga sun saki fursunoni 58 ba tare da an harba ko da harsashi guda daya ba. Sakamakon matakan gina amana, an sake ’yantar da fiye da mutane 80 a cikin makonni kadan da suka biyo baya. Yau, adadin ya haura fursunoni 500, duk an sako su lafiya lau, babban tarihi a tsawon fafutukar zaman lafiya ta Jihar Kaduna.

“Zaman lafiya da muke ginawa a Kaduna ya ta’allaka ne a kan tattaunawa, ba mulki da karfi ba,” in ji Gwamna Uba Sani.

 

Mahimmin Sauyi: Tattaunawa da Bukatu

Nasara ta fara bayyana ne a zagaye na biyu na zaman tattaunawa tsakanin kwamitin musamman na ONSA–Kaduna da shugabannin Kungiyoyin makamai. Wannan ba irin tattaunawar da aka saba ba ce, amma an gina ta ne a kan gaskiya da fahimtar juna.

‘Yan bindiga sun gabatar da sharuddan su na zaman lafiya sun kuma hada da;

1. Sake bude kasuwannin yankunan.

2. Samun damar ‘ya’yansu na zuwa makarantu

3. Birnin Gwari, Giwa da Kudancin Kaduna su samu kulawa a asibitoci.

Maimakon a yi watsi da wadannan bukatu a matsayin dabara kawai, gwamnati ta gane cewa su ne ainihin bukatun ’yan kasa da ke tsakanin neman rayuwa ko mika wuya. Gwamna Sani ya gaggauta amincewa a bude kasuwanni, tare da umartar a dawo da al’amuran rayuwa yadda suka saba a yankunan da abin ya shafa.

An samu Sakamakon nan take kuma a bayyane. Hanyoyin da suka zama tamkar matattu a Giwa da Birnin Gwari yanzu sun cika da ayyuka. Matafiya sun tabbatar da cewa mutum na iya wucewa ta wadannan yankuna “ko da da daddare” kuma ya isa lafiya, abin da ba zai yiwu a tunanin mutane ba shekaru biyu da suka gabata.

 

Limaman addini, Turji da Muhallin Al’amura

A gefe guda, wasu malaman addini karkashin jagorancin Sheikh Musa Yusuf (Asadus Sunnah) sun bayyana a bainar jama’a cewa sun gudanar da tarurruka a cikin dajin da sanannen shugaban ’yan fashi Bello Turji da wasu kwamandojinsa.

A cewar rahoton jaridar Banguard ta ranar 5 ga Agusta, 2025, malamin ya bayyana cewa “an saki fursunoni 32 kuma an mika makamai” bayan tattaunawar da aka yi da Turji.

Wannan rahoton yana da mahimmanci ga tsarin sulhun Kaduna domin yana nuna yadda masu ruwa da tsaki na cikin gida da hukumomin yankin ke kirkirar damar shimfida zaman lafiya a matakin jiha: sakin fursunoni, ba da izini ga manoma su koma gonakinsu, da takaitaccen sauke makamai wanda ke rage cutarwa kai tsaye a kasa.

 

Daga ’Yan Fashi zuwa Masu wanzar da Zaman Lafiya

Watakila shaidar da ta fi daukar hankali game da wannan sauyi ita ce bayyanar tsoffin ’yan fashi da suka tuba, yanzu sun zama masu kiyaye zaman lafiya a yankuna da suka taba tarwatsawa.

A Birnin Gwari, tsohon fitaccen dan fashi ‘Jan Bros’ yanzu yana sintiri a cikin dazukan da shi da mutanensa suka buya a da, yana tabbatar da cewa babu sababbin barazana.

A Kudu maso Gabashin Kaduna, wani sanannen mutum da ake kira ‘Yellow 1 Million’ ya zama mai sulhu kuma mai fafutukar wanzar da zaman lafiya, sannan yana hani da tashin hankali.

Wadannan sauye-sauyen na iya zama kamar abin mamaki, kuma su ne sahihan ayyukan shirin zaman lafiya da ya yi kokarin tattaunawa maimakon kawar da su gaba daya. Kamar yadda wani masani kan tsaro ya ce, “Kaduna ta yi abin da wasu jihohi ke mafarkin yi, ta mayar da tsoffin abokan gaba zuwa masu rike da ragamar zaman lafiya.”

 

Samfurin Zamani lafiya

Samfurin Zaman Lafiyar Kaduna ba gwaji ne na lokaci daya ba, tsari ne mai dorewa, mai ci gaba da sauyawa.

A makon jiya ma, kwamitin musamman ya sake gudanar da taro, a wannan karon tare da shugabannin ’yan fashi, dagatai daga Kajuru, Kauru, Kagarko da Kachia, tare da sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi.

Taron, wanda Asadus Sunnah ya jagoranta, ya mayar da hankali kan karfafa abin da aka riga aka cimma da kuma hana komawar rikici.

Wannan ci gaba na tattaunawa, amincewa da sa ido, su ne suka bambanta hanyar Kaduna da wadancan yunkurin zaman lafiya na dan lokaci da aka yi a wasu sassan Nijeriya.

 

Farfado Da Tattalin Arziki: Zaman Lafiya Na Haifar Da Riba

Zaman lafiya ya fara haifar da sakamako a zahiri. Ayyukan noma a Giwa da Birnin Gwari da Kudancin Kaduna sun kai matakin da ya fi kowanne shekaru da suka gabata. Kasuwancin shanu, wanda matsalar tsoro ya dakile a da, ya sake farfadowa — yanzu manyan motoci 20 zuwa 30 na dauke da shanu suna bi ta hanyoyin da matsalar tsaro ya kange tsawon shekaru da dama.

Farfadowar kasuwanci ba wai ta tattalin arziki kadai ba ce; alama ce da ke nuna cewa an maido da mutunci da darajar al’umma.

“Duk wani kasuwa da aka sake bude nasara ce a kan tsoro,” in ji Gwamna Sani. “Duk wani yaro da ya koma makaranta shaida ce cewa tattaunawa na iya kayar da rashin bege.”

 

Samar Da Zaman Lafiya Ba Tare da Makami Ba A Yankunan Afrika

Sabon salon wannan aiki na Kaduna ya wuce iyakokin Nijeriya wajen tasiri. A fadin Afirka, al’ummomi sun dade suna gwagwarmaya da rashin nasarar amfani da karfin soja kadai. Daga shirin Afuwa na Yankin Neja Delta zuwa sulhun bayan kisan kare dangi a Rwanda, har zuwa tattaunawar da aka yi da rundunar Lord’s Resistance Army a Uganda — darasin daya ne: zaman lafiya na dindindin ba ya fitowa daga bakin bindiga ana gina shi ne ta hanyar shigar da kowa, tausayi da adalci.

Gwamna Uba Sani da tawagar ONSA sun daidaita wannan basira zuwa yanayin gida. Hanyar da suka bi ta nuna cewa ikon tattaunawa, idan an gina shi kan amincewa kuma doka ta tallafa, na iya dawo da zaman lafiya ko a wurare mafi tsauri.

 

Ka’idoji Uku Da Tushen Zaman Lafiyar Kaduna:

Ana samun zaman lafiya ne tare da tafiya da al’umma, ba wai a umarce su daga ofisoshin gwamnati ba. Sarakunan gargajiya, matasa, mata, da jami’an tsaro suna zama ne a tebur daya.

2. Shigar da Kowa cikin Tattalin Arziki: Farfado da kasuwanni, makarantu da asibitoci yana cire tushen da ke bai wa ’yan tawaye karfi.

3. Amincewa ta Hanya Mai Dorewa: Tattaunawa ta ci gaba, ba na lokaci-lokaci ba. Shigar ONSA yana tabbatar da rikon kwakwalwar hukuma da ci gaba a tsakanin hukumomi.

Wadannan ka’idojin sun yi daidai da abin da Babban Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkar, Nuhu Ribadu, ya lura, wanda a wata hira da Channels TB a ranar 29 ga Yuli, 2025, ya yaba da hadin gwiwar dabarar rashin amfani da karfi kuma ya tabbatar da cewa “daruruwan fursunoni sun sami ‘yanci a fadin kasa ta hanyar ayyukan zaman lafiya da aka tsara tare.” Ribadu ya kuma bayyana cewa “A yanzu samun sahihan bayanan sirri, shigar al’umma, da dakatar da harkokin ta’addanci na dindindin” maimakon kawai kai farmaki da kama mutane.

 

Mataki na gaba

Ko da yake har yanzu akwai wasu barazanar lokaci-lokaci, tubalan zaman lafiya a Kaduna sun fi karfi fiye da da. Gwamna Uba Sani ya tsaya tsayin daka: “Ba mu ayyana nasara ba; muna ayyana sadaukarwa. Kowace rana da muka kiyaye wannan zaman lafiya rana ce da ta kara kusantar da mu ga dorewar kwanciyar hankali ga al’ummarmu.”

Kalmominsa yanzu suna yaduwa a cikin Birnin Gwari da sauran sassan Kudancin Kaduna da Giwa wadanda a da ake jin harbin bindiga, amma yanzu aka maye gurbinsu da dariyar yara da kuma walwalar kasuwanci.

 

Darasi Ga Nijeriya Da Afirca

Dabarun wanzar da Zaman Lafiyar Kaduna shi ne shaida wa mai rai cewa ko a cikin mafi hadarin yankin Nijeriya, zaman lafiya na iya samu ta hanyar tattaunawa kuma da hanyar ci gaban al’umma. Yana tabbatar da gaskiya mai sauki ba tare da tsorata dan’Adam ba.

Ta hanyar hadin gwiwa da Ofishin Mashawarcin Tsaron Kasa, Gwamna Uba Sani ya nuna cewa yakin neman zaman lafiya ba a kan dazuka ko hare-haren sama ake samun nasara ba, sai ta dabaru cikin zukatan da suke shirye su yafe, shugabanni kuma su shirya su saurari al’ummar da suke da karfin gwiwar sake ginuwa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Rahotonni Jerin Gwarazan Taurarinmu! November 7, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025 Rahotonni Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
  • Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah
  • Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
  • Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba
  • Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu
  • Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu
  • Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai
  • Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu