Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
Published: 17th, September 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800.
Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta.
Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je wurin yayar tata, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karbar bashinta na N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai tankiyar da ta fara a matsayin ƙaramin sabani ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta riƙe kayan marigayiyar har ta faɗi ƙasa.”
“Abin takaici, duk da an garzaya da marigayiyar asibiti don samun kulawar gaggawa, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba.”
Bayan faruwar lamarin, rundunar ta ce ta kama wadda ake zargi kuma tana tsare da ita a halin yanzu, yayin da bincike ke ci gaba.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, domin ta girbi abin da ta shuka.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa.
Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko.
“A gaskiya tafiyar shekara ɗaya da ta wuce ta yi mana matuƙar wuya. Mun zo mu sauya tsarin kasuwancin man ƙasa. Amma wasu na ganin mun raba su da hanayar cin abinci bakinsu,” in ji shi.
’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati BaYa ci gaba da cewa, “Amma abin da muka yi shi ne mun sa Najeriya da nahiyar Afirka gaba ɗaya su yi alfahari.”
Ɗangote ya ce matatar ta riga ta fitar da lita biliyan 1.8 na man fetur zuwa ƙasashen waje cikin watanni uku da suka gabata, sannan tana da isasshen ƙarfi wajen cika buƙatar cikin gida.
Ya ce tun daga fara aikin matatar a watan Satumbar 2024, dogayen layukan man fetur da suka fi shekaru 50 ana fama da su a Najeriya sun zama tarihi.
Ɗangote ya ƙara da cewa farashin fetur ya sauka daga kusan Naira 1,100 zuwa N841 a wasu jihohi, kuma da zarar sabbin motocin gas (CNG) masu dakon mai sun fara aiki a duk faɗin ƙasar, rage farashin zai fi tasiri.
Ya kuma bayyana cewa sabbin motocin CNG 4,000 za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.
“Ba mu kore kowa daga aiki ba, sai dai muna ƙara samar da ayyuka,” in ji shi.
Ɗangote ya zargi masu harkar mai da haɗa kai da ’yan kasuwa na cikin gida da na waje da ƙoƙarin hana nasarar matatar.
“Yadda aka hallaka masana’antar yadi, haka suke ƙoƙarin kashe matatar mu,” in ji shi.
A kan zargin cewa bai wadatar da ƙasa da fetur ba, sai ya mayar da martani da cewa: “Idan ba mu da ƙarfin samar da mai, me ya sa muke fitarwa zuwa ƙasashen waje?”
Ya kuma yi ba’a ga Ƙungiyar Ma’aikatan Mai (NUPENG) wadda ta ce rage farashin fetur na matatar Dangote “kyautar Girka ce.” Dangote ya ce: “Ko da kuwa kyautar Girka ce, ai kyauta ce, za ta kuma ci gaba da kasancewa.”
Ya jaddada cewa abin da Najeriya ke buƙata yanzu shi ne kare masana’antunta, domin ci-gaban tattalin arziki da kuma rage dogaro da shigo da kaya daga waje.