Aminiya:
2025-09-19@18:01:16 GMT

An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe

Published: 19th, September 2025 GMT

Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin.

Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas

Ya bayyana cewa wani mutum mai suna Aliyu Chindo ne, ya ba su aikin cire idanun mamacin, tare da yi wa kowannensu alƙawarin Naira 500,000.

Sai dai ya ce bayan kai masa sassan jikin, Chindo ya gudu ba tare da ya biya su ba.

Nan take jami’an tsaro suka cafke su.

An gano cewa sun tono kabarin wani tsoho mai shekaru 85, Mallam Manu Wanzam, wanda aka binne a ranar 9 ga watan Satumba a maƙabartar Gadam Arewa da ke Ƙaramar Hukumar Kwami.

Kakakin NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya bayyana sunayen sauran da aka kama: Adamu Umar (22), Umar Jibrin Aboki (21), Abdullahi Umar Dauda (17), Muhammed Isa Chindo (28), da Manu Sale (23).

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da neman Aliyu Chindo da ya tsere.

Kwamandan hukumar a jihar, Jibrin Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani,” tare da tabbatar da cewa za su gurfanar da waɗanda suka kama a kotu bayan kammala bincike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kabari

এছাড়াও পড়ুন:

Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka

Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
  • Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar
  • ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
  • Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista
  • ’Yansanda Sun Kama Sojan Gona Da Motocin Sata 3 A Jigawa
  • Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja