Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi
Published: 20th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar mutuwar mutane 58 sanadiyyar kamuwa da cutar amai da gudawa (kwalara) inda ta gano sabbin masu dauke da cutar mutane 258, wanda aka samu a kananan hukumomi 14 cikin 20 na jihar.
Duk shugaban da bai yi aiki ba bai kamata a sake zaɓarsa ba — Jonathan An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a KalabaMataimakin gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Auwal Jatau ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da cutar kwalara na jiha, da kuma kwamitin kwararru kan yaki da cutar.
Jatau ya bukaci mambobin kwamitocin da su tunkari ayyukan da aka dora musu cikin kishi da kwarewa da kuma hanzari.
Mataimakin Gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin ya koka kan yadda cutar kwalara da ta sake barkewa, kuma tana ci gaba da janyo asarar rayuka, da kuma kawo cikas ga harkokin rayuwa da kuma kawo kalubalen ga tsarin kiwon lafiyar jihar.
Ya ce, cutar kwalara na daya daga cikin manyan cututtuka da ke barazana ga lafiyar al’umma, duk da kokarin da gwamnatin jihar da takwarorinta ke yi na shawo kan cutar.
Jatau ya bayyana cewa, kafa kwamitoci yana da mahimmanci wajen cimma manufofin da ake so.
“Ana iya yin rigakafin wadannan bullar cutar tare da daukar matakan da suka dace,, da kuma ci gaba da inganta tsaftar ruwan sha tsaftar muhalli, da tsaftar jiki.”
A kan haka ne ake sa ran kwamitin zai yi aiki tare da kungiyoyin hadin gwiwa don shawo kan matsalar.
Ya ce, Jihar Bauchi ta mayar da hankali kan barkewar cutar kwalara da kuma fitar da dabarun rigakafin cutar kwalara na dogon lokaci tare da tsare-tsare da tsare-tsare na kasa da kasa kan tsare-tsaren dakile cutar kwalara a Najeriya da yin rigakafi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Kwalara cutar kwalara
এছাড়াও পড়ুন:
An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa na ƙasa.
Shugaban sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya shigo daga jihar Ribas ne musamman domin amfani da taron siyasar da aka shirya wajen yin sata.
Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a NajeriyaYa ce jami’ansu sun kama shi ne bayan sun lura da motsinsa da ya sa suka zarge shi. Bayan bincike, sai suka gano wayoyi 17, kudi N91,000, da kuma katunan ATM da dama a cikin jaka da yake dauke da ita.
Alagba ya kara da cewa, Francis ya shaida musu cewa yana aiki tare da wasu abokan laifi da suka tsere yayin kamun.
Ya kuma bayyana cewa kafin a kama shi, sun riga sun kwashe sama da N400,000, sannan daya daga cikin wadanda suka gudu yana da karin wayoyi da sauran kayayyakin da suka sace.
Shugaban sa-kai din ya gargadi masu aikata laifuka da su guji shiga Bayelsa, yana mai cewa jami’ansa sun samu horo na musamman kan tattara bayanan sirri, lura da halayen jama’a da kuma tsaron taruka.