Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote
Published: 23rd, September 2025 GMT
Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta tabbatar da cewa ta samu takardun kotu da ke hana mambobinta sayar da tikiti ko duk wani yunƙuri da zai kawo tsaikon al’amura a Matatar Ɗangote.
Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja ranar Talata, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Gas (PENGASSAN).
Akporeha ya ce kungiyar tana mutunta doka, kuma za ta bari shari’a ta yi aikinta har sai an kammala duk wani sha’ani a kotu.
“Kamar yadda kowa ya sani, Ɗangote ya kai mu kotu, kuma yanzu mun samu umarnin kotu da ya hana mu sayar da tikiti ko datse duk wata hanya zuwa harabar matatarsa. Za mu ci gaba da kiyaye wannan doka, mu bar shari’a ta yi aikinta,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito yadda a makon da ya gabata, Kotu Masana’antu da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi da ya hana kungiyar shiga yajin aiki ko tilasta wa direbobin manyan motoci rajista da ita.
Alkalin kotun, Mai Shari’a E.D. Subilim, ya bayar da wannan umarni, wanda ya shafi Kungiyar Direbobin Motoci Masu Dakon Man Fetur, inda ya hana su rufe hanyoyin Najeriya ko dakile ayyukan Matatar Ɗangote, MRS Oil Nigeria Plc, da MRS Oil and Gas Company Ltd.
A yayin taron, NUPENG ta musanta zargin cewa tana karɓar ₦50,000 daga manyan motocin da ke ɗaukar mai a daffo-daffo .
“Ba NUPENG kaɗai ke aiki a daffo-daffon ba. Akwai wasu ƙungiyoyi da ke aiki a wuraren. Don haka batun cewa NUPENG tana karɓar N50,000 ba gaskiya ba ne,” in ji Akporeha.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matatar Dangote
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Tana Maraba Da Kwararru Daga Bangarori Daban Daban Na Kasa Da Kasa Su Zo Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp