Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa
Published: 21st, September 2025 GMT
Jami’ar European American University ta musanta bai wa fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, digirin girmamawa na dokta.
A jiya Asabar ce dai wani bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta ya nuna yadda ake karrama Rarara da digirin girmamawa a wani bikin yaye ɗalibai da aka gudanar a otel ɗin NICON Luxury da ke Abuja.
Sai dai cikin wani saƙo da ta fitar a shafinta a ranar Asabar, jami’ar ta ce sam ba ta da hannu a lamarin kuma ba da izininta ba.
Jami’ar ta bayyana cewa, ba ta taɓa ba da izinin gudanar da taron karramawa ko taron yaye ɗalibai a wannan wurin da kuma wannan ranar ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an shirya taron ne ta hanyar yaudara, ba tare da sanin jami’ar ba kuma ba tare da amincewarta ba.
Haka kuma, ta ce waɗanda suka shirya taron, sun yaudari jama’a “da nuna kamar suna wakiltar Jami’ar European-American.
“Wannan kuwa ƙarya ce tsagwaronta, domin ba su da wata alfarma ko izini, balle kuma su karɓi kuɗi a madadin jami’ar.
Jami’ar European-American ta ƙara da cewa, “ba ta taɓa bai wa Dauda Kahutu Rarara, Alhaji Ahmed Saleh Jnr., Mustapha Abdullahi Bujawa ko Tarela Boroh wata girmamawar digirin Doktora ba.
“Dukkan waɗanda jami’ar ta karrama da digiri na gaskiya suna cikin rajistar dalibai da aka yaye wacce ake iya dubawa a hukumance.”
Tun bayan ɓullar labarin digirin girmamawa da aka yi wa fitaccen mawaƙin siyasar, mutane da dama suke tofa albarkacin bakinsu, inda da dama suka taya shi murna, a ɓangare guda kuma wasu suka ƙalubanci lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dauda Kahutu Rarara Digirin Girmamawa Jami ar European American digirin girmamawa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
‘Yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Pankshin Kudu, Laven Denty, a gidansa da ke unguwar Dong na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A makon da ya gabata ma, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin unguwar Dong, inda suka yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), da kuma ɗalibin Jami’ar Jos.
Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025Masu garkuwar da mutanen sun shiga gidan iyalan Solomon Dansura, da misalin ƙarfe 10 na dare inda suka tafi da baƙinsa guda biyu a lokacin.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin jihar ko kuma tabbaci daga rundunar ‘yansandan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp