An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki
Published: 19th, September 2025 GMT
Gwamnatin jihar Sakkwato ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare guda shida kan zargin karbar kudi daga hanun dalibai na bisa ka’ida ba.
Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala ne ya amince da dakatarwar.
Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin FilatoAna dai zargin dakatattun shugabannin makarantun ne da karɓar kudin jarabawa daga hannun daliban da suka kammala karamar sikandare (JSS) ba tare da izinin gwamnati ba, wasu daga cikinsu kuma ana zargin su sun walaƙanta shugabanni da ke sama da su.                
      
				
Shugabannin da aka dakatar sun hada da shugabar makarantar mata ta Nana da Makarantar gwamnati ta Gagi (GDSS) da makarantar sakandare ta Mana da Kwalejin Giginya da Baisic ta Mana da sakandaren Silame.
Kwamishinan ya kuma kafa kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Namakka Tukur don su bincika zarge-zargen da aka yi wa shugabannin da aka dakatar.
Kwamishina, a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Muhammad Iya, ya fitar ya umarci shugabannin su mika ragamar makarantun ga hannun mataimakansu na mulki nan take.
“Ma’aikatar ilmi za ta ci gaba da yin tsayin daka ta tabbatar da tarbiya da rike amana da gaskiya a dukkan makarantun jihar Sakkwato,” a cewarsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36.
Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024.
BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon tattalin arziki mai zaman kansa.
A bangaren haraji, jihar ta samu naira biliyan 25.46 a 2024, ƙaruwa ce ta kusan kashi 15% daga naira biliyan 22.16 a shekarar da ta gabata. Har ila yau, kuɗaɗen FAAC sun ƙaru da sama da kashi 239%, daga naira biliyan 65.28 a 2023 zuwa biliyan 221.42 a 2024.
Rahoton ya kuma yi hasashe kan habakar kuɗaxen shiga marasa haraji, inda aka samu ƙaruwa sosai a bangaren lasisi, kuɗin biyan takardu da wasu hanyoyin samun kuɗaɗe. Misali, kuɗaɗen lasisi sun tashi da fiye da kashi 5,900% a shekarar 2023.
A ɓangaren kashe kuɗi, musammam a fannin lafiya da ilimi, rahoton ya nuna ƙarin kuɗaɗen da gwamnati ta zuba, duk da cewa akwai ƙalubalen ingantacciyar aiwatarwa. Jimillar kashe kuɗin lafiya ta tashi daga naira biliyan 4.29 a 2022 zuwa biliyan 11.88 a 2024, inda kashe kuɗi kan mutum ɗaya ya ninka fiye da biyu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA