Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-04@09:47:47 GMT

Jihar Jigawa Ta Halarci Babban Taro Kan Kasuwancin Halal A Malaysia

Published: 19th, September 2025 GMT

Jihar Jigawa Ta Halarci Babban Taro Kan Kasuwancin Halal A Malaysia

Tawagar gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahun sauran kasashe da suka halarci taron kasa da kasa na Halal da ke gudana a Malaysia (MIHAS), domin neman jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki.

Tawagar karkashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Kiwo, Farfesa Abdurrahman Salim Lawal, ta hada da Dr.

Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Hukumar Zamanantar da Harkar Noma ta Jihar Jigawa, da kuma Hajiya Aisha Sheik Mujaddadi, Darakta-Janar ta Hukumar Inganta Zuba Jari ta Jihar.

Tuni dai tawagar ta halarci taruka daban-daban yayin isar su kasar ta Malaysia, ciki har da taron Halal Certification Convention, taron kasuwancin Halal na duniya, da  MIHAS Power Talk kan zuba jari ta hanyar Halal, da kuma zaman tattaunawa kan kasuwar Halal da bada shaida.

 

Farfesa Lawal ya ce Jihar Jigawa na son ta zama cibiyar samar da kayayyakin Halal a yammacin Afirka, ta hanyar nuna ƙarfin ta a bangaren noma, musamman kiwo da kuma amfanin gona.

Ya kara da cewa manufar ita ce samar da haɗin gwiwa da kamfanonin Malaysia, hukumomin gwamnati, da shugabannin masana’antun da ke samar da kayayyakin Halal a fannonin sarrafa nama da noman da aka tabbatar da Halal.

“Shigar mu cikin MIHAS wani bangare ne na jajircewar wannan gwamnati wajen bambance hanyoyin samun kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi. Mun yi imani cewa haɗin gwiwa da bayanan da muka samu daga wannan taro za su taimaka wajen jawo jari da kuma samar da damar arziki ga al’ummarmu.” In ji shi.

Tawagar ta kuma gudanar da tarurruka da dama tare da manyan masu ruwa da tsaki na Malaysia domin tattauna batutuwan zuba jari, musayar fasaha, da kuma shirye-shiryen ƙarfafa ƙwarewa.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Malaysia Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka November 3, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje 100 Ga Waɗanda Rikici Ya Shafa A Jihar
  • Gwamna Namadi Ya Yaba Da Tasirin Shirin NG-CARES A Jihar Jigawa
  • An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
  • Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi
  • Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda