Sudan: Hamedti ya yi rantsuwar shugabantar gwamnati mai kishiyantar gwamnatin kasar
Published: 31st, August 2025 GMT
Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar.
Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran Reuters ya kasa tabbatar da inda yake.
Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo.
A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF ya shelanta kafa abin da ya kira gwamnatin zaman lafiya da hadin kai, wadda ya kira gwamnatin Sudan ta gaskiya.
A ranar 26 ga watan Maris, kungiyar ‘yan tawayen Sudan ta Rapid Support Forces (RSF) da kungiyoyin da ke kawance da ita, suka rattaba hannu kan kundin tsarin mulkin rikon kwarya da ke share fagen kafa gwamnati mai kiyantar juna da gwamnatin kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba August 30, 2025 Larijani: Iran Tana Adawa Da Juya Akalar Siyasar Yankin Daga Wasu Masu Son Baba-Kere August 30, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Maraba Da Matakin Wasu Kasashen Turai Na Nuna Kyamarta Zaluncin Isra’ila August 30, 2025 Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila August 30, 2025 Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza August 30, 2025 Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki August 30, 2025 Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya August 30, 2025 Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar August 30, 2025 Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai August 30, 2025 E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da takunkuman MDD a kan Iran August 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
Hukumar kare hakkin bil’adam dake karkashin MDD ya sanar da cewa tana sa ido akan kashe-kashe da rashin adalcin da ake yi a karkashin zaben shugaban kas ana kasar Tanzania. Tun a ranar Larabar da ta gabata ne dai da ake zaben rikici ya barke a kasar sabod kin amincewar ‘yan hamayya akan yadda zaben zai gudana ba tare da manyan ‘yan takara ba. Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan ce dai babbar ‘yar takara. Babbar jam’iyyar adawa ta sanar da cewa fiye da mutane 700 ne aka kashe a fadin kasar da ake Zanga-zanga. Shugaban ofishin hukumar kare hakkin bil’adama na MDD Seif Magango ya sanar da cewa; Sun karbi rahoranni daga majiya mai tush akan cewa a kalla an kashe mutane 10. Hukumar ta yi kira ga jami’an tsaron kasar ta Tanzania da su daina amfani da karfi a inda bai dace ba, daga cikin har da amfani da makamai akan masu Zanga-zanga. Haka nan kuma sun yi kira ga masu Zanga-zanga da su yi a cikin ruwan sanyi. Ita kuwa kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta ce nata rahoton ya tabbatar mata da cewa an kashe abinda bai kasa mutane 100 ba. Tuni dai aka kafa dokar ta baci da hana zirga-zarga a babban birnin ksar Darus-salam, ana kuma rufe hanyoyin sadarwa na interten daga lokaci zuwa lokaci. Har ila yau MDD tana yin kira da a saki dukkanin wadanda ake tsare da su.Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci