Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa DagaKotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya
Published: 24th, September 2025 GMT
Kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya
Kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
Sanarwar wadda wakilin gwamnati kuma ministan sadarwa na Burkina Faso, Benguendé Gilbert Ouédraogo ya karanta, ta ce: Gwamnatocin Burkina Faso, Jamhuriyar Mali, da Jamhuriyar Nijar, wadanda suka kafa kungiyar hadin kan kasashen Sahel, sun sanar da ra’ayin jama’a na wannan kungiyar da al’ummar duniya kan matakin da suka dauka na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya nan take.
A baya, kasashen uku sun bayyana kotun da aka ambata a matsayin “kayan cin zali ga kasashen Afirka” tare da nuna aniyarsu ta ficewa daga kotun ta ICC da kuma kafa takwararta ta yankin.
Wadannan kasashen sun tabbatar da cewa: Dalilin ficewarsu daga kotun shine son zuciya na wannan cibiya. Wakilan kasashen Afirka uku ne suka yanke shawarar ficewa daga yarjejeniyar Rome a wani zama na musamman na ministocin shari’a na kungiyar Sahel.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo September 23, 2025 Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba September 23, 2025 Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida September 23, 2025 Jakadan Amurka Ya Amince Da Cewa Amurka Tana Nufin Hada Yaki Tsakanin Sojojin Lebanon Da Hizbullah September 23, 2025 ‘Yan Gwagwarmaya Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza September 23, 2025 Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu September 23, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi September 23, 2025 Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ficewa daga
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah
Wani sabon kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka ya nemi a hana ’yan kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore bizar shiga Amurka.
Kudurin, wanda dan majalisa Christopher Smith ya gabatar a ranar Talata, ya kuma bukaci kwace kadarorin mambobin kungiyar.
An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwaWannan na daga cikin matakan da gwamnatin Amurka ke ɗauka don dakile abin da ta kira take hakkin ’yancin addini ga Kiristocin Najeriya.
Kudirin dai na neman hukunta mutane da ƙungiyoyi da ke da hannu ko goyon baya wajen take hakkin ’yancin addini mai, a ƙarƙashin dokar kasa da kasa ta IRFA.
Christopher ya yaba wa Shugaba Trump bisa sake ayyana Najeriya a matsayin Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman, yana mai ambato rahotannin ci gaba da hare-hare kan al’ummomin Kirista a sassan ƙasar.
Kudirin ya kuma ambaci ’yan ta’adda Fulani da ke kai hare-hare a jihohin Binuwai da Filato a cikin kungiyoyin da ake sa’ido a kansu, wani matsayi da Amurka ke warewa ga ’yan ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da ake zargi da take hakkin addini.
Sauran irin wadannan kungiyoyin da aka ayyana a baya a ƙarƙashin dokar sun haɗa da Boko Haram, ISWAP, ISIS-Sahel, Taliban da kuma Houthi.
Idan aka amince da kudirin, zai bai wa hukumomin Amurka damar hana biza da kuma kulle kadarorin mutanen da ke da alaƙa da waɗannan ƙungiyoyi.
An gabatar da kudirin ne bayan watanni na kiraye-kirayen yin hakan daga ’yan majalisar dokokin Amurka da ƙungiyoyin Kiristoci masu tsattsauran ra’ayin.
Shugaban Amurka Donald Trump dai ya yi zargin ana yi wa Kiristoci a Najeriya kisan kiya, amma gwamnatin kasar ta yi fatali da zarge-zargen inda ta kira shi a matsayin na karya.