Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a Gaza, Mohammed Sinwar
Published: 31st, August 2025 GMT
Ƙungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar Mohammed Sinwar, wanda aka daɗe ana ɗauka a matsayin jagoranta a Gaza.
Wannan tabbaci ta Hamas ta bayar na zuwa ne fiye da watanni uku bayan Isra’ila ta ce ta kashe shi a wani harin sama.
Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara Xi na karɓar baƙuncin taron SCO a ChinaHotunan da Hamas ta fitar ranar Asabar sun nuna Sinwar tare da wasu manyan shugabannin siyasa da na soji, waɗanda aka bayyana a matsayin “shahidan kwamitin soji.
Mohammed Sinwar, shi ne ƙanen Yahya Sinwar wanda Isra’ila ke zargi da jagorantar harin ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra’ila, rikicin da har yanzu wutarsa ke ƙara ruruwa.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa Mohammed Sinwar ya jagoranci kwamitin sojin Al-Qassam Brigades bayan mutuwar kwamanda Mohammed Deif.
Tun dai a ranar 13 ga watan Mayun da ya gabata ne rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe Mohammed Sinwar, wanda a watan Yuni kuma aka gano gawarsa a wani rami ƙarƙashin Asibitin Turai da ke Khan Yunis.
A watan Oktoban 2023 ne Hamas ta ƙaddamar da hari a Kudancin Isra’ila, inda sama da mutum 1,219 suka mutu.
Hakanan daga cikin mutum 251 da Hamas ta yi garkuwa, rahotanni na nuna cewa akwai aƙalla mutum 47 da har yanzu take tsare da su a Gaza, ciki har da kusan 20 da ake ganin suna raye.
Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ta tabbatar da sahihancin alƙaluman, ta ce martanin da Isra’ila ta mayar ya jawo asarar rayuka masu yawa a Gaza, inda ma’aikatar lafiya ta Gazan ta ce sama da mutane 63,371 — mafi yawansu fararen hula — sun mutu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila Mohammad Sinwar Yahya Sinwar Mohammed Sinwar
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.
A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp