Dembele ya lashe kyautar balon d’or ta bana
Published: 23rd, September 2025 GMT
Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Ousmane Dembélé ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana.
Balon d’or dai ita ce lambar yabo mafi girma a duniyar ƙwallon kafa wacce ake bai wa gwarzon ɗan wasa na shekara.
.উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faransa Lamine Yamal
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno Birtaniya za ta amince da ƙasar FalasɗinuGwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba.
“Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai domin kawo ƙarshen barazanar ta’addanci.”
A nasa jawabin, Rabiu Baushe, ya gode wa gwamnan bisa wannan tallafi, inda ya bayyana cewa motocin da baburan za su ƙara musu ƙarfi wajen yin sintiri da shawo kan hare-hare a yankunan karkara.
Ya kuma yi alƙawarin cewa ƙungiyar PROHAN za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a dukkanin sassan Jihar Gombe.