Aminiya:
2025-09-24@08:31:50 GMT

An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu

Published: 21st, September 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Enugu ta tanadi tukwuicin naira miliyan goma ga duk mutumin da ya taimaka aka kama waɗanda ake zargi da kashe fitaccen limamin cocin Katolika, Matthew Eya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa tabbatar da alƙawari da Kwamishinan Labarai, Malachy Agbo, ya fitar ranar a Asabar.

NAF ta hallaka Boko Haram 32 a Borno Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa

Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka.

Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun yi wa limamin kwanton-ɓauna wanda suke harbe a yayin da yake kan hanyar komawa gida daga yankin Enugu Urban.

Limamin cocin mamba ne a Cocin Nsukka Catholic Diocese, wadda ta tabbatar da kisan nasa.

A sanarwar da Mista Agbo ya fitar, ya ambato gwamnatin Enugu tana “yin Allah wadai da kakkausar muryar” bisa “mummunan kisan” da aka yi wa limanin cocin.

“Gwamnatin Enugu tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan limanin cocin, da Catholic Diocese ta Nsukka, da kuma mabiya ɗarikar Katolika baki ɗaya bisa wannan iftila’i,” a cewar kwamishinan.

Ya bayyana makasan a matsayin “matsorata” waɗanda suka aiwatar da kisan “rashin imani”, inda ya sha alwashin cewa gwamnati za ta kama ‘yan bindigar da suka yi wannan aika-aika.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Enugu Mathew Eya

এছাড়াও পড়ুন:

Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza

A Italiya dubun dubatan mutane ne suka fito kan tituna domin yin Allah wadai da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a Gaza.

Wannan gangami ya zo ne a ranar da wasu kasashe da dama ke shirin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a Majalisar Dinkin Duniya, bayan Birtaniya, Australia da Canada a ranar Lahadi.

Duk da cewa Italiya ba ta da niyyar daukar irin wannan matakin a yanzu, A birnin Rome, fiye da mutane 20,000, ne  suka taru dauke da tutocin Falasdinu domin nuna goyan bayansu.

An gudanar da zanga-zangar a wasu garuruwa da dama a fadin kasar, ciki har da Milan inda mutane 50,000 suka shiga zanga zangar in ji masu wadanda suka shirya ta.

Saidai Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, an artabu tsakanin masu zanga-zangar da ‘yan sandan Italiya a tsakiyar birnin Milan.

Sauran zanga-zangar sun gudana a Turin (arewa), Florence (tsakiya), Naples, Bari, da Palermo (kudu).

Baya ga haka bayanai sun ce ‘yan darikar Katolika sun shirya taron nuna goyon baya da addu’a a babban birnin Italiya a yammacin yau Litinin.

A cewar wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a, kasha 63.8% na ‘yan Italiya suna ganin halin da ake ciki na jin kai a Gaza ya kasance “mai tsanani,” kuma kasha 40.6% na son amincewa da kasar Falasdinu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025   Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani  Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi                          September 22, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya
  • Larijani: Iran Tana Nazarin Shawarwarin Turai Da Na Rasha Domin Kare Muradunta
  • Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi
  • An kama ɗan sandan bogi a Kano
  •  HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
  • ’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda
  • Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza
  • ’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno