Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (KSSQAA), ta gargadi masu makarantu masu zaman kansu kan kara kudin makaranta ba tare da samun amincewar gwamnatin jihar a hukumance ba. A wata takarda mai kwanan ranar 7 ga Satumba, 2023, wacce Mercy Bainta Kude, Daraktar Sashen Makarantu masu zaman kansu ta sanya wa hannu a madadin Darakta-Janar, Hukumar ta jaddada cewa “babu wani ko wata mai makaranta da zai ko za ta kara kudin makaranta ko inganta makarantar ​​ba tare da amincewar KSSQAA ba.

” Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna Umurnin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin rage kudaden makaranta a makarantun mallakar jihar tare da tabbatar da bin ka’idojin da suka dace a fannin ilimi. A cewar sanarwar, masu gudanar da makarantu masu zaman kansu dole ne su cika wasu sharuɗɗa kafin su nemi ƙarin kuɗin makaranta. Waɗannan sharuɗɗa sun haɗa da shaidar cewa, daga ƙarin farko zuwa na biyu,dole sai an ɗauki aƙalla shekaru uku, ƙungiyar iyayen yara da Malamai ta amince da ƙudurin buƙatar ƙarin kuɗin makarantar a yayin taronta sannan babban daraktan makarantar ya rubuto takarda a hukumance ta neman ƙarin kuɗin makarantar. Kude ta ƙara gargaɗin masu makarantu da su bi waɗannan sharuɗɗa, inda tace, bin dokar ya zama dole don tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: makarantu masu

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
  • Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
  • Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri