Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu
Published: 21st, September 2025 GMT
Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Tun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar.
Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba ta ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas ba kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na watan Satumba.
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, Starmer zai yi jawabi ga al’umma kan matsayarsa, gabanin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya, inda ƙasashe 10 ciki har da Faransa za su amince da kafa ƙasar ta Falasɗinu.
Sai dai Amurka da Isra’ila sun soki matakin, suna bayyana shi a matsayin saka wa Hamas duk da harin da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Su ma ƙasashen Portugal da Canada da Australia sun ce za su amince da ƙasar Falasɗinun a cikin wannan mako.
Daga gobe Litinin ce sama da shugabannin ƙasashe 140 ne za su hallara a birnin New York domin taron shekara-shekara na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Matsalar jinƙai da ta addabi yankin Falasɗinu za ta kasance a kan gaba a tattaunawar da za ta gudana a taron na bana.
Shugaba guda da ba zai halarci taron a zahiri ba shi ne shugaban Falasɗinawa, Mahmud Abbas, wanda Amurka ta hana biza tare da waɗansu jami’ansa.
A karo na musamman, babban zauren ya kaɗa ƙuri’a a ranar Juma’a domin bai wa Abbas damar gabatar da jawabi ta hanyar bidiyo, yayin da jakadan Falasɗinu zai wakilce shi a cikin ɗakin taron.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Birtaniya Isra ila ƙasar Falasɗinu
এছাড়াও পড়ুন:
Kashim Shettima Ya Isa New York Halartar Taron UNGA Na 80
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York, Amurka, domin halartar taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28, 2025. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabin Nijeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa da tarukan a gefe da dama.
Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da mara baya ga tsarin haɗin gwuiwa tsakanin ƙasashe, ciki har da yunƙurin samun kujerar dindindin a Majalisar Tsaron MDD bisa matsayar haɗin kan Afrika, wato Ezulwini Consensus. Ya ce Shettima zai kuma bayyana sabbin manufofin Nijeriya na rage hayaƙin da ke gurbata muhalli bisa yarjejeniyar Paris.
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan ManomaA yayin da aka tarɓe shi, Shettima ya samu rakiyar ministoci da gwamnoni ciki har da na Kaduna, Uba Sani, wanda ya ce halartar Nijeriya a UNGA zai ƙara jawo masu zuba hannun jari ga tattalin arzikin ƙasar, musamman a fannin ma’adanai, da noma da ilimin sana’o’in dogaro da kai. Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Olajumoke Oduwole, ta ce Nijeriya za ta yi amfani da taron wajen tallata shirin Nigeria Investment Day, da zai mayar da hankali kan ma’adanai, da sadarwa da kuma fasaha.
Rahotanni sun nuna cewa Shettima zai kuma shiga taron kwamitin zaman lafiya na Tarayyar Afrika, tare da ganawa da shugaban gwamnatin Sudan da sauran manyan jami’ai, domin jaddada matsayar Nijeriya kan rikicin Gabas ta Tsakiya, Sudan da gabashin Kongo. Wannan dai na nuna yunƙurin Nijeriya na ƙara taka rawar gani a harkokin diflomasiyya da ci gaban nahiyar Afrika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp