Yiwuwar yajin aikin direbobin tankar mai kan rikicin Matatar Dangote
Published: 8th, September 2025 GMT
Najeriya na iya shiga cikin matsalar ƙarancin man fetur daga yau Litinin, muddin Gwamnatin Tarayya ba ta warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai (PTD) ta ƙarƙashin NUPENG da kamfanin Matatar Mai ta Dangote ba.
Direbobin sun sanar da shiga yajin aiki saboda shirin kamfanin Ɗangote na fitar da motoci 4,000 da ke amfani da gas ɗin CNG domin kai mai kai tsaye ga kasuwa ba tare da direbobin da ke ƙarƙashin NUPENG ba.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa wannan tsari zai rusa ayyukan dubban direbobi, ya hana ’yancin kafa ƙungiya kuma ya haifar da “mulkin danniya” a harkar rarraba man fetur.
Gwamnati ta shiga tsakaniMinistan Ƙwadago da Ayyuka, Muhammad Maigari Ɗingyadi, ya tabbatar a jiya Lahadi cewa ma’aikatarsa ta gayyaci dukkan ɓangarorin zuwa taron sasanci a Abuja.
Yadda dawowar makarantu ta zo mana cikin tsadar rayuwa — Iyaye NAJERIYA A YAU: Yadda Ilimi Ke Ƙara Tsada Yayin Komawar Yara MakarantaYa roƙi NUPENG ta dakatar da yajin aikin da aka shirya, tare da kira ga Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) ta janye gargadin da ta ba wa ƙungiyoyin ma’aikata na shiga yakin aiki direbobin domin nuna goyon baya.
“Ina roƙon su su ba da dama ga zaman lafiya. Ina tabbatar musu za a warware lamarin cikin ruwan sanyi,” in ji shi cikin wata sanarwa.
Sai dai majiyoyi daga NUPENG sun ce za su tsaya daga yajin aikin har sai sun ji sakamakon zaman. “Saboda mutunta shigar gwamnati tsakani, mun dakatar domin sauraron gwamnati da fatan samun mafita,” in ji wani jigo a ƙungiyar.
Zargin cin zarafiA wata sanarwa da shugabancin NUPENG ya fitar, ƙungiyar ta zargi kamfanin Ɗangote da hana sabbin direbobi shiga kowace ƙungiya. Ta ce hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki da ƙa’idojin ƙwadago na duniya.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa duk da irin goyon bayan da ta ba wa kamfanin yayin gina matatar, yanzu yana neman mallakar harkar rarrabawa da karya gasa da kuma “ninka farashin da ya ga dama.”
“Ba za mu amince a rusa rayuwar ’ya’yanmu ba. Za mu tsaya tsayin daka wajen kare ’yancin direbobi,” in ji shugabannin NUPENG, Kwamared Williams Akporeha da Afolabi Olawale.
Rarrabuwar kawunaSai dai batun ya jawo saɓani a tsakanin direbobi. Wata ƙungiya mai suna Direct Trucking Company Drivers Association (DTCDA) ta ce ba ta da alaƙa da NUPENG, don haka ba ta cikin yajin aikin. Shugabanta, Barista Enoch Kanawa, ya bayyana cewa ƙungiyarsu za ta ci gaba da aiki.
Amma NUPENG ta yi watsi da su, tana mai cewa ƙungiyar ta Kanawa ƙirƙira ce ta kamfanin Ɗangote domin hana direbobi shiga NUPENG.
“Barista ba direba ba ne, kuma babu wani sashe na PTD da ya balle daga NUPENG,” in ji ta.
Haka kuma, shugabannin sassa huɗu na PTD daga Kaduna, Warri, Fatakwal da Legas sun fito da sanarwa suna kira ga direbobi su yi watsi da umarnin yajin aiki, suna kiran shi da “rahin hankali kuma mai cutarwa.”
Magoya bayan yajin aikinDuk da wannan rarrabuwar kawuna, Ƙungiyar Masu Gidajen Man Fetur (PETROAN) ta nuna goyon bayanta ga yajin aikin.
Shugabanta, Dakta Billy Gillis-Harry, ya sanar da dakatar da ɗebo mai daga rumbunan ajiya na tsawon kwanaki uku daga gobe Talata, a matsayin gargaɗi.
Ya ce matakin na nufin tabbatar da gasa mai kyau a kasuwa tare da kare al’umma daga mallakar rarraba mai a hannun kamfani guda. “Yajin da ake shirin yi doka ce kuma cikin lumana za a yi shi,” in ji shi.
Tsoron ƙarancin maiTuni masana da masu kasuwa suka fara gargadin cewa idan ba a sami sulhu ba nan da sa’o’i, matsalar ƙarancin mai za ta bazu a faɗin ƙasa.
Matatar Ɗangote dai ta shirya fara jigilar mai kai tsaye tun daga 15 ga watan Agusta, sai dai ta samu tsaiko saboda matsalolin jigilar motocin daga China da kuma saɓani da ƙungiyoyi.
Duk da haka, wasu daga cikin motocin CNG sun iso Najeriya, abin da ya nuna shirin ya kusa farawa.
Masana na gargaɗiMasu sharhi a masana’antar sun ce wannan rikicin ya fito da babbar tambaya kan rawar da Ɗangote zai taka a ɓangaren mai.
Duk da ana sa ran matatar za ta rage dogaro da shigo da man fetur, akwai fargabar ta mamaye harkar rarrabawa da kuma raunana sauran masu ruwa da tsaki.
Masanin harkokin ƙwadago, Dakta Chris Agbo, ya ce, “Abin da ake bukata shi ne daidaita sha’awar jari-hujja da kuma kare ’yancin ma’aikata. Idan ba haka ba, rikice-rikice za su ci gaba.”
Kiran gwamnatiA ƙarshen mako, Ministan Ƙwadago ya sake roƙon NUPENG da NLC su janye yajin aikin da suka shorya.
“Tun da mun shiga tsakani, ina roƙo a ba da dama. Za mu tabbatar an warware lamarin ba tare da lalata harkokin mai ba,” in ji shi.
Sai dai majiyoyi a cikin NUPENG sun shaida cewa matakin su na gaba zai dogara da yadda taron sasancin zai kaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗangote Ƙwadago Yajin aiki yajin aikin
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
An zabi Doro ne bayan naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Doro a matsayin ƙwararren masani da ke da fiye da shekaru 20 na ƙwarewa a fannoni da dama ciki har da aikin asibiti, gudanar da harkokin magunguna, da jagoranci a Nijeriya da Birtaniya.
An haifi Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a Kwall, ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau. Yana da digiri a fannin magunguna da shari’a, MBA a dabarun kasuwanci na IT, da kuma digiri na biyu a fannin aikin lafiya mai zurfi (Advanced Clinical Practice).
Da amincewar da aka yi masa a yau, ana sa ran Bernard Doro zai rantse a matsayin ɗan majalisar zartarwa (FEC) a zaman majalisar ministoci na gaba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA