Iran Tace IAEA Ta Amince Da Sabuwar yarjeniya Da Ita
Published: 11th, September 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia.
A lokacinda yake jawabin hadin guiwa ta tokwaransa na kasar ta Tunisia.
Kafin haka dai Aragchi ya yada zango a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya gana da Rafael Grossi shugaban hukumar IAEA, suka kuma rattaba hannu kan sabuwar yarjeniya da hukumar, ta yadda hulda tsakaninsu zata kasance bayan hare-haren da HKI da Amurka suka kai wa cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar ta Iran.
A dayan bangaren kuma kasashen turai 3 Jamus Faransa da kuma Ingila, sun ki amincewa da sabuwar yarjeniyar, Aragchi ya ce, abin mamaki ne.
Kasashen uku dai suna kokarin ganin Hukumar ta IAEA ta kara takurawa JMI kan shirinta na Makamashin nukliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Ta Kai Hari Da Makamai Mazu Linzami A Wasu Yankuna A Yamen September 11, 2025 Shugaban Nijeriya Ya Bada Da Umarnin Karya Farashin Kayan Abinci . September 11, 2025 Iran Tayi Tir Da Harin HKI A Yamen Da Kuma Kashe Yan Jarida September 11, 2025 Ana Gab Da Kulla Yarjejeniyar Iskar Gas Tsakanin Iran Da Kasar Rasha. September 11, 2025 Kasar Ghana Ta yi Tir Da Harin Da Isra’ila Takai A Kasar Qatar September 11, 2025 Araghchi :Yarjejeniya da IAEA zata dore idan ba’a dauki mataki kan Iran ba September 11, 2025 “Kasashen Larabawa ma basu tsira ba daga hare-haren Isra’ila” (Naim Qassem) September 11, 2025 Faransa : Mutane 250,000 suka shiga zangar zangar ‘’a Toshe komai’’ inji CGT September 11, 2025 MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike September 11, 2025 Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci September 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai wa jiragen ruwa a yankin Caribbean da Pacific, wanda ya kasance keta dokokin kare hakkin dan adam na duniya.
“An ruwaito cewa an kashe mutane sama da 60 a jerin hare-haren da sojojin Amurka ke kai wa jiragen ruwa a Caribbean da Pacific tun farkon watan Satumba, wadanda ake zargin suna da hannu a safarar miyagun kwayoyi, a cikin wani yanayi da ba su da hujja a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji Volker Turk a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.
Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana hare-haren a matsayin “abin da ba za a yarda da shi ba” kuma ya bukaci Washington da ta “kawo karshen irin wadannan hare-hare ta kuma dauki dukkan matakan da suka dace don hana kisan gillar da ake yi wa mutanen da ke cikin wadannan jiragen ruwa ba bisa ka’ida ba, ba tare da la’akari da laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba.”
Amurka ta yi ikirarin cewa wadannan ayyuka wani bangare ne na yaki da safarar miyagun kwayoyi da ta’addanci.
Duk da haka, Turk ya nuna cewa yaki da safarar miyagun kwayoyi a kan iyakoki “al’amari ne na tilasta bin doka.”
“Dangane da ƙarancin bayanai da hukumomin Amurka suka bayyana a bainar jama’a, da alama mutanen da ke cikin jiragen ruwan da aka kai hari ba su da wata barazana ga rayukan wasu, kuma ba a yi amfani da karfin soji mai tsanani a kansu ba a karƙashin dokokin kasa da kasa,” in ji shi.
Volker Turk ya yi kira da a “yi bincike mai zaman kansa cikin sauri, kuma ya yi kira ga Amurka da ta yaki fataucin na haramtacciyar hanya ta hanyar kamawa, da gurfanar da wadanda ake tuhuma cikin adalci, da kuma bin ka’ida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci