An Gabatar Da Fim Mai Taken Shen Zhou 13 A Kasar Birtaniya
Published: 21st, September 2025 GMT
A gun liyafar murnar cika shekaru 76, da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da ofishin jakadancin Sin dake Birtaniya ya shirya a jiya Jumma’a 19 ga wata, an gabatar da wani fim mai taken Shen Zhou 13, fim din kasar Sin na farko da aka dauka kai-tsaye a sararin samaniya kuma bisa fasahar 8K, wadda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar wato CMG ya tsara.
Wannan ne karo na farko da aka gabatar da fim din a kasashen waje.
Al’ummun kasar Birtaniya daga bangarori daban daban, da jami’an diflomasiyyar kasa da kasa dake Birtaniya, gami da Sinawa dake zaune a kasar sama da 400, sun halarci liyafar.
Wasu ’yan saman jannati uku na kumbon Shenzhou-13, wato Zhai Zhigang, Wang Yaping, da Ye Guangfu, su ne suka dauki wannan fim, wanda ya shaida yadda suke aiki, da rayuwa na tsawon watanni shida a tashar binciken sararin samaniya ta Sin. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya? November 2, 2025
Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025
Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025