Sin Da Amurka Na Iya Cimma Manyan Nasara Tare In Ji Shugaba Xi
Published: 20th, September 2025 GMT
A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Daga nan sai ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin kasarsa da Sin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing
Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing.
Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800.
Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun ci gaba cikin sauye-sauye”, da “amfani da sarrafa sabbin fasahohi”, da kuma “kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha da sauye-sauyen yanayin yaki”. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp