Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80
Published: 20th, September 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci babban taron mahawara na MDD karo na 80 a birnin New York na kasar Amurka, tsakanin ranakun 22 zuwa 26 ga watan Satumban nan.
A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, firaminista Li, zai kuma halarci wasu ayyuka da Sin za ta shirya, ciki har da taron manyan jami’ai dangane da shawarar bunkasa ci gaban duniya da Sin ta gabatar, kana zai gana da babban magatakardar MDD, da jagororin kasashe masu ruwa da tsaki kan batun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp