Aminiya:
2025-09-24@08:34:23 GMT

Ballon d’Or: Wa zai lashe kyautar 2025?

Published: 22nd, September 2025 GMT

Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na  bana.

A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya.

Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa.

Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin.

An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina

Ga jerin manyan ’yan wasa biyar da aka fi ganin suna da damar lashe ta bana:

Ousmane Dembélé – (PSG, Faransa)

Ousmane Dembélé ne ke kan gaba a jerin masu fafatawa.

Dembele ya ta rawa gani wajen kai PSG ga nasarar lashe kofuna uku – gasar Ligue 1, Coupe de France da kuma kofin Zakarun Turai na farko a tarihin kulob ɗin.

Ya zura kwallaye 21 tare da taimaka wajen cin wasu shida, musamman a muhimman wasanni.

Wannan ne yasa ake kallonsa a matsayin babban ɗan fafatawa.

2. Lamine Yamal – (Barcelona, Sifaniya)

Matashin ɗan shekara 17 zuwa 18 ya yi abin mamaki a wannan kakar.

Yamal ya yi fice a gasar La Liga da kuma Copa del Rey inda ya zura kwallaye 18 tare da taimakawa wajen cin kwallaye da bayar da dama aka ci wasu 21.

Kwarewarsa da kwazo suka sa ake kallon shi tamkar fitacciyar tauraruwa ta gaba.

Sai dai kuma duk da haka, rashin nasara a Gasar Zakaraun Turai na iya rage masa ƙuri’u.

3. Raphinha – (Barcelona, Brazil)

Shi ma Raphinha yana daga cikin manyan ’yan wasan da suka yi fice a bana.

Ya zura kwallaye 34 tare da bayar da damaa ka zura wasu 22 a muhimman wasanni.

Barcelona ta yi nasara a gida, kuma gudummawarsa ta zama abin yabo.

Amma duk da haka, ya na iya fuskantar kalubale wajen daga irin bambanci tsakaninsa da sauran taurarin Barcelona.

4. Vitinha – (PSG, Portugal)

Vitinha na daga cikin ɗan tsaka-tsaki da aka yaba da rawar da ya taka a PSG.

Shi ke tsare tsakiya, yana rarraba kwallo da samar da daidaito tsakanin tsaro da hari.

Duk da cewa ba shi da yawan kwallaye ko taimako irin na ’yan wasan gaba, gudummawarsana da matuƙar muhimmanci.

Sai dai irin wannan rawar kan kananan wurare na iya zama mai ƙarancin tasiri ga masu kada ƙuri’a.

5. Mohamed Salah – (Liverpool, Masar)

Salah ya ci gaba da zama ginshiƙi a Liverpool inda ya taimaka musu su lashe Gasar Firimiyar Ingila da kwallaye da dama da kuma taimakon cin wasu. A matsayinsa na ɗan wasa da ya dade yana taka rawar gani, yana da daraja a idanun masu jefa kuri’a.

Amma rashin kai Liverpool mataki mai nisa a Champions League na iya rage darajarsa a wannan karon.

Abubuwan da ke iya tabbatar da nasara?

Masu shirya gasar sun ce abubuwan da ake la’akari da su wajen zabar Gwarzon Dan Wasan su ne: Hazikancinsa shi kadai, dabi’unsa da iya yanke hukunci da kuma gudummawa ga abokan wasansa dai saurnasu kamar haka:

Lashe manyan kofuna musamman Champions League. Nuna kwazo a manyan wasanni kamar na karshe ko na kusa da karshe. Yawan kwallaye da taimako na da tasiri ga masu jefa kuri’a. Nasarorin kasa-kasa ma na iya ƙara daraja. Salonsa da kuma iya wasa ba tare da keta ba, kamar yadda matashin Yamal ya zo da sabon salo, na iya tasiri. Yiwuwar ba-zata

A halin yanzu, ana kallon Ousmane Dembélé a matsayin babban wanda ke iya lashe wannan babbar kyauta, yayin da Lamine Yamal ke biye masa.

Raphinha, Vitinha da Mohamed Salah kuwa suna nan a sahun gaba suna jiran rarrabuwar ƙuri’u wanda hakan ke iya sa su kai bantensu.

Duk da haka, Ballon d’Or ya saba zuwa abubuwan ban mamaki; duk wani ɗan wasa mai tasiri — mai tsaron raga, mai tsaron gida, ko wani fitacce —na iya mamaye sahun gaba idan ya nuna bajinta a ƙarshen kakar. 

Kazalika kokarin dan wasa na karshe-karshe musamman a Champions League ko wasannin kasashe na iya sauya kuri’un.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kwallaye Raphinha Yamine Yamal

এছাড়াও পড়ুন:

Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa DagaKotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya

Kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya

Kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.

Sanarwar wadda wakilin gwamnati kuma ministan sadarwa na Burkina Faso, Benguendé Gilbert Ouédraogo ya karanta, ta ce: Gwamnatocin Burkina Faso, Jamhuriyar Mali, da Jamhuriyar Nijar, wadanda suka kafa kungiyar hadin kan kasashen Sahel, sun sanar da ra’ayin jama’a na wannan kungiyar da al’ummar duniya kan matakin da suka dauka na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya nan take.

A baya, kasashen uku sun bayyana kotun da aka ambata a matsayin “kayan cin zali ga kasashen Afirka” tare da nuna aniyarsu ta ficewa daga kotun ta ICC da kuma kafa takwararta ta yankin.

Wadannan kasashen sun tabbatar da cewa: Dalilin ficewarsu daga kotun shine son zuciya na wannan cibiya. Wakilan kasashen Afirka uku ne suka yanke shawarar ficewa daga yarjejeniyar Rome a wani zama na musamman na ministocin shari’a na kungiyar Sahel.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo September 23, 2025 Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba September 23, 2025 Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida September 23, 2025 Jakadan Amurka Ya Amince Da Cewa Amurka Tana Nufin Hada Yaki Tsakanin Sojojin Lebanon Da Hizbullah September 23, 2025 ‘Yan Gwagwarmaya  Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza September 23, 2025  Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu September 23, 2025  HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi September 23, 2025   Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa DagaKotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya
  • Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025.
  • Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025
  • Jadawalin ‘Yan Wasa 30 Na Farko A Kyautar Ballon D’or Ta Bana
  • Dembele ya lashe kyautar balon d’or ta bana
  • Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa
  • Ballon d’Or: ’Yan wasa 5 da ke iya lashe kyautar 2025 
  • Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro
  • Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?