Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan
Published: 22nd, September 2025 GMT
Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a birnin Al-Fashir na kasar Sudan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kira harin a matsayin ” keta dokokin jin kai na kasa da kasa.”
Ta kuma jaddada bukatar gaggauta dakatar da kai hare-hare kan fararen hula da muhimman ababen more rayuwa a kasar Sudan, tare da bayyana cewa dole ne a warware rikicin kasar ta hanyar “tattaunawa tsakanin ‘yan Sudan.”
Iran ta bayyana juyayinta ga wadanda lamarin ya ritsa dasu tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Sama da mutane 70 ne aka kashe a wani harin da aka kai da jirghi marar matuki da dakarun sa kai na (RSF) suka kai a wani masallaci da ke Al-Fashir a ranar Juma’a, in ji sojojin Sudan da masu aikin ceto a yankin.
lamarin na ranar Juma’a ya nuna wani sabon tashin hankali a yakin basasa na shekaru uku tsakanin sojojin Sudan da RSF.
Tun daga watan Afrilun 2023, yakin Sudan ya kashe dubunnan mutane tare da raba wasu miliyan 12 da muhallansu.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin a matsayin daya daga cikin mafi muni a duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi September 22, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 22, 2025 Ministan Harkokin Waken Falasdinu Ta Yi Kira Ga Karin Kasashe Su Amince Da Samuwar Kasarta September 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wani masallaci
এছাড়াও পড়ুন:
Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran.
Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran, amma shigarsu ta dogara ne da manufofin siyasar Iran.
Ya ce: “Damar da suke da shi tana da kunci sosai, don haka tawagar hukumar IAEA tana da ‘yan sa’o’i kadan ko ‘yan kwanaki don sanin ko yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai za ta yiwu, kuma wannan ita ce hanyar da dukan bangarorin biyu suke nema.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya September 24, 2025 Imam Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo September 23, 2025 Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba September 23, 2025 Sauye-Sauyen Siriya A hannun Amurka Da Aika’ida September 23, 2025 Jakadan Amurka Ya Amince Da Cewa Amurka Tana Nufin Hada Yaki Tsakanin Sojojin Lebanon Da Hizbullah September 23, 2025 ‘Yan Gwagwarmaya Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza September 23, 2025 Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu September 23, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi September 23, 2025 Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci