Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025.
Published: 23rd, September 2025 GMT
An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa.
Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa dan wasan da ya nuna gwaninta a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da dan wasan ya bayar ga kungiya da kuma kasarsa.
Tun farko an fitar da jerin ‘ƴan wasa 30 cikin wadanda ake sa ran za su lashe kyautar.
Dembele ya taka rawar gani wajen taimakon kungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan karshe a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi.
Ya zura ƙwallo 21 a wasa 29 da ya buga a gasar Ligue 1, inda ya karkare gasar a matayin wanda ya fi zura kwallo, sannan ya lashe kyautar gwarzon dan’wasan gasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ballon d’Or: ’Yan wasa 5 da ke iya lashe kyautar 2025
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana.
A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya.
Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa.
Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin.
An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a KatsinaGa jerin manyan ’yan wasa biyar da aka fi ganin suna da damar lashe ta bana:
Ousmane Dembélé – (PSG, Faransa)Ousmane Dembélé ne ke kan gaba a jerin masu fafatawa.
Dembele ya ta rawa gani wajen kai PSG ga nasarar lashe kofuna uku – gasar Ligue 1, Coupe de France da kuma kofin Zakarun Turai na farko a tarihin kulob ɗin.
Ya zura kwallaye 21 tare da taimaka wajen cin wasu shida, musamman a muhimman wasanni.
Wannan ne yasa ake kallonsa a matsayin babban ɗan fafatawa.
2. Lamine Yamal – (Barcelona, Sifaniya)Matashin ɗan shekara 17 zuwa 18 ya yi abin mamaki a wannan kakar.
Yamal ya yi fice a gasar La Liga da kuma Copa del Rey inda ya zura kwallaye 18 tare da taimakawa wajen cin kwallaye da bayar da dama aka ci wasu 21.
Kwarewarsa da kwazo suka sa ake kallon shi tamkar fitacciyar tauraruwa ta gaba.
Sai dai kuma duk da haka, rashin nasara a Gasar Zakaraun Turai na iya rage masa ƙuri’u.
3. Raphinha – (Barcelona, Brazil)Shi ma Raphinha yana daga cikin manyan ’yan wasan da suka yi fice a bana.
Ya zura kwallaye 34 tare da bayar da damaa ka zura wasu 22 a muhimman wasanni.
Barcelona ta yi nasara a gida, kuma gudummawarsa ta zama abin yabo.
Amma duk da haka, ya na iya fuskantar kalubale wajen daga irin bambanci tsakaninsa da sauran taurarin Barcelona.
4. Vitinha – (PSG, Portugal)Vitinha na daga cikin ɗan tsaka-tsaki da aka yaba da rawar da ya taka a PSG.
Shi ke tsare tsakiya, yana rarraba kwallo da samar da daidaito tsakanin tsaro da hari.
Duk da cewa ba shi da yawan kwallaye ko taimako irin na ’yan wasan gaba, gudummawarsana da matuƙar muhimmanci.
Sai dai irin wannan rawar kan kananan wurare na iya zama mai ƙarancin tasiri ga masu kada ƙuri’a.
5. Mohamed Salah – (Liverpool, Masar)Salah ya ci gaba da zama ginshiƙi a Liverpool inda ya taimaka musu su lashe Gasar Firimiyar Ingila da kwallaye da dama da kuma taimakon cin wasu. A matsayinsa na ɗan wasa da ya dade yana taka rawar gani, yana da daraja a idanun masu jefa kuri’a.
Amma rashin kai Liverpool mataki mai nisa a Champions League na iya rage darajarsa a wannan karon.
Abubuwan da ke iya tabbatar da nasara?Masu shirya gasar sun ce abubuwan da ake la’akari da su wajen zabar Gwarzon Dan Wasan su ne: Hazikancinsa shi kadai, dabi’unsa da iya yanke hukunci da kuma gudummawa ga abokan wasansa dai saurnasu kamar haka:
A halin yanzu, ana kallon Ousmane Dembélé a matsayin babban wanda ke iya lashe wannan babbar kyauta, yayin da Lamine Yamal ke biye masa.
Raphinha, Vitinha da Mohamed Salah kuwa suna nan a sahun gaba suna jiran rarrabuwar ƙuri’u wanda hakan ke iya sa su kai bantensu.
Duk da haka, Ballon d’Or ya saba zuwa abubuwan ban mamaki; duk wani ɗan wasa mai tasiri — mai tsaron raga, mai tsaron gida, ko wani fitacce —na iya mamaye sahun gaba idan ya nuna bajinta a ƙarshen kakar.
Kazalika kokarin dan wasa na karshe-karshe musamman a Champions League ko wasannin kasashe na iya sauya kuri’un.