Leadership News Hausa:
2025-09-19@09:41:21 GMT

2027: Su Wane Ne Ke Tsoron Guguwar Makinde A Jam’iyyar  PDP

Published: 19th, September 2025 GMT

2027: Su Wane Ne Ke Tsoron Guguwar Makinde A Jam’iyyar  PDP

Idan aka yi ɗan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba ɗaya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne ɗan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027.

Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake kira da “Star Boy”, ya kafa kansa a matsayin jagoran PDP a yankin yamma, tafiyarsa zuwa kujerar gwamna ba ta zo masa da sauƙi ba.

Kafin shekarar 2019, Makinde ya tsaya takarar kujerar Sanatan Oyo ta Kudu a shekarar 2007, amma ya sha kaye a hannun Kamoru Adedibu. Duk da wannan rashin nasara ta farko, bai karaya ba. A 2010, ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya sake neman kujerar Sanata na Oyo ta Kudu a zaɓen 2011, amma ya sha kaye a zaɓen fid da gwani a hannun sanatan da ke riƙe da kujerar a lokacin.

A 2014, Makinde ya nemi tikitin PDP domin takarar gwamnan Jihar Oyo a zaɓen 2015. Amma a watan Disamba 2014, bayan kammala zaɓen fid da gwani, jam’iyyar ta hana shi samun tikitin gwamna. Duk da haka, Makinde ya ci gaba da jajircewa bisa burinsa na yi wa al’ummar Oyo hidima, yana mai dagewa kan hangen nesansa na ci gaban jihar.

A ranar 29 ga Satumba 2018, Makinde ya zama ɗan takarar gwamna na PDP a babban zaɓen 2019 a Jihar Oyo, bayan ya samu ƙuri’u 2,772 a zaɓen fid da gwani. Kamar yadda ya bayyana a lokacin: “Mutanen Oyo ne suka yanke shawara a 2019. Ba mu da wani uba a siyasa. Babu wanda ya ɗauki nauyinmu. Babu wanda ya ba mu ko sisin kobo don mu kai ga nasara.”

Yau, Makinde ya shafe sama da shekaru shida daga cikin shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya amince masa ya yi a matsayin Gwamnan Jihar Oyo. Ko da yake bai bayyana niyyarsa game da 2027 ba tukuna, tursasawa da kira gare shi da ya shiga fagen takarar na ƙara ƙarfi a kullum.

Masu nazarin siyasa na ci gaba da sa ido kan matakan da zai ɗauka a nan gaba yayin da wa’adin gwamnatinsa na biyu ke gab da ƙarewa. Wata makoma ce da dama a cikin jam’iyyar mai mulki, da ma wasu daga cikin PDP, ke ganin abin tsoro ne da damuwa.

A 2019, Makinde bai dogara da wani uban gidan siyasa ba, amma ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Oyo. A yau kuma, mutane da dama a faɗin ƙasar na ganin cewa, idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, akwai yiwuwar ya maimaita irin “sihirin nasara” da ya yi a Oyo.

Da yawa na ganin cewa dama tana gefensa daga zaɓen fid da gwani na PDP har zuwa babban zaɓen shugaban ƙasa a 2027. Ko da yake bai fito fili ya sanar da niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa ba tukunna, amma shahararsa da ke ƙara bunƙasa a cikin PDP da wajenta, na nuna irin ƙarɓuwar da yake samu a matakin ƙasa, wanda ya sa ake kallonsa a matsayin babban ƙalubale ga duk wani ɗan takarar APC a gaba.

Gwamna Makinde, saɓanin wasu a cikin jam’iyya, ya tsaya tsayin daka kan aƙidar PDP, ya tsaya tare da jam’iyyar a lokutan ƙalubale.

A lokacin da manyan jiga-jigan PDP suka gudu suka koma APC da sunan neman haɗuwa da “cibiya mai ƙarfi”, Makinde bai bar jam’iyyar ba, maimakon haka ya tallafa mata da dukiya da albarkatu.

A yau, farin jinin Gwamna Seyi Makinde ya kai kololuwa, yana ratsawa cikin dukkanin shiyyoyin ƙasar shida. Wannan ya sanya jam’iyyar mai mulki cikin fargaba, yayin da salon jagorancinsa ke ƙara yin ƙarfi har zuwa wajen nahiyar Afirka.

An gwada farin jinin Gwamna Makinde a ranar 16 ga Agusta, 2025, lokacin da aka gudanar da zaɓen cike gurbi na majalisar tarayya a Ibadan North Federal Constituency. Ɗan takarar PDP, Fola Oyekunle, ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u 18,404, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na APC, Adewale Olatunji, wanda ya samu ƙuri’u 8,312.

An gudanar da wannan zaɓe ne domin cike gurbin rasuwar Hon. Olaide Akinremi ta bari.

Sakamakon ya nuna nasara mai ƙarfi ga PDP a Jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Makinde, tare da zama shaida kan tasirinsa da kuma gagarumin farin jininsa a jihar, abin da ke sa abokan hamayyarsa a fagen siyasa cikin fargaba.

A ƴ an kwanakin nan ma, wata ƙungiyar masu goyon bayan PDP mai suna Reset Lagos PDP ta yi kira ga al’ummar Inyamurai (Igbos) a faɗin ƙasar da su haɗa kai wajen mara wa Gwamna Makinde baya domin ya karɓi mulki a shekarar 2027.

Mai shirya ƙungiyar, Dr Adetokunbo Pearse, wanda shi ma shugaban National Support Group for Makinde ne, ya shaida wa manema labarai cewa Makinde ya bambanta da sauran masu sha’awar takara, kuma yana da gaskiya da sha’awar ci gaban al’ummar Igbo a zuciyarsa.

Ya ce, “Shi ne kaɗai ya nuna sha’awa a tsayawa takara, kuma ya yi bajinta sosai a matsayin gwamnan Jihar Oyo. Ya shiga siyasa ba tare da dogaro da kuɗin gwamnati ba, tun daga jami’a, saɓanin yawancin ƴ an siyasa da ke shigowa da komai a hannunsu sannan su fara dogaro da dukiyar gwamnati.”

A gefe guda, shugaban reshen Legas na Igbonine Great Peoples Assembly, Elder Okezie Anyanwu, ya bayyana cewa zaɓen 2027 ba zai kasance yadda aka saba ba, inda ya yi kira ga Inyamurai da ke Legas da su haɗa kai da PDP, wacce ya bayyana a matsayin jam’iyya mai ingantattun tsare-tsare a Legas.

Ya ce, “Dalilin da ya sa na ke tare da PDP shi ne ita ce kawai jam’iyya da ke da tsari a kowane sashi na Nijeriya. Kuma tubalin PDP ya ta’allaƙa ne kan nagarta da gaskiya saɓanin waɗannan jam’iyyun da suka fito daga baya. Ina kira ga kowa da kowa da ya kada ƙuri’a yadda ya dace.”

Idan za a iya tunawa wata ƙungiya mai suna ‘Nigeria Youths Awareness Group Makinde 2027’  (NYAG Makinde 2027), a watan Mayu, yayin taron manema labarai a Kano kan hasashen siyasar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ta bayyana a fili cewa tana alfahari da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin mutumin da zai iya ciyar da Nijeriya gaba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa dukkanin ƴ an Nijeriya masu kishin dimokuraɗiyya ya kamata su haɗa kai a bayan Makinde ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, domin tabbatar da samun tikitin tsayawa takara.

Yayin ganawa da manema labarai a Kano, Alhaji Lawal Abdullahi, Sakataren Ƙasa na ƙungiyar, ya bayyana cewa: “Mun haɗu a matsayin ƙungiyoyi daban-daban kuma mun amince mu yi tafiya tare domin Seyi Makinde ya zama shugaban ƙasa a 2027. Mu jirgin da ke tafiya ne, babu wani abu da zai iya tsayar da mu sai mun cimma burinmu na shugabancin Seyi Makinde.”

Gwamna Seyi Makinde tun da farko ya kasance mai jituwa da Arewacin ƙasar nan a harkokinsa na siyasa, tattalin arziƙi da kuma zamantakewa. A lokacin da rikicin jam’iyyar PDP ya yi tsanani, Makinde a tattaunawarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar daga Arewa ya taka rawar gani wajen sasanta al’amura domin kuɓutar da PDP daga rugujewa.

Makinde bai taɓa ɓoye matsayinsa kan batutuwan jam’iyya ba. Yayin hira da ƴ an jarida kwanan nan bayan taron tunawa da cikar shekara 10 da naɗin Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi, ya yi tsokaci kan ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga PDP. Ya ce: “Siyasa wasa ne na muradu.

Ban yi imani cewa ficewarsa zai bar wani giɓi ga PDP a matsayin jam’iyya ba. PDP wata ƙungiya ce mai ƙarfi. Muna da ƴ ancin shiga da fita. Duk wanda yake riƙe PDP da hannunsa, gara ya fice.

Abin da ya kamata mu fahimta shi ne: ƴ an wasa suna zuwa suna tafiya, gwamnoni suna zuwa suna tafiya, shugabanni suna zuwa suna tafiya, amma jiharmu da ƙasarmu za su ci gaba da wanzuwa.”

A nasa ɓangaren, Hon. Dare Adeleke, wanda shi ne mai ba wa Gwamna Makinde shawara kan harkokin Mazaɓu na Tarayya, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki APC na cikin firgici da tasirin Makinde a siyasar ƙasar kafin 2027.

Adeleke ya ce: “APC na cikin tsananin tsoro da yiwuwar tikitin Makinde a ƙarƙashin PDP. Sun san cewa idan ya tsaya takara, hakan na iya zama mummunan hasashe ga mulkinsu mai cike da gazawa, mulki da ake iya cewa shi ne mafi ban takaici a tarihin Nijeriya.”

Shaharar Makinde a faɗin ƙasar ta zama babban ƙalubale ga waɗanda ya doke sau biyu a Jihar Oyo. Suna fargabar cewa zai maimaita irin wannan nasara idan ya shiga fafatawar shugaban ƙasa a 2027.

Ga jiga-jigan PDP da ke da wannan ra’ayi, Gwamna Makinde na da ƙwarewa da cancantar da za su iya kai jam’iyyar ga nasara a babban zaɓen 2027.

Yayin da tafiyar 2027 ke ƙara bayyana a fili, ƴ an Nijeriya na jiran ganin fitattun ƴ an siyasa sun fito da kundin ayyukansu da zai nuna irin mulkin da suka yi da kuma abin da za su iya kawowa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a zaɓen fid da gwani Gwamna Makinde bayyana cewa a Jihar Oyo

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi

Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da sauyin musayar kuɗaɗen waje.

An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m

A cewarsa, aƙalla gidaje miliyan 19.7 (sama da mutum miliyan 70) aka sanya a Rajistar Tsarin Tallafa Wa Talakawa, kum tallafin ya kai ga gidaje miliyan 15.

“Zuwa yanzu, gidaje miliyan 8.5 sun samu aƙalla Naira 25,000 sau ɗaya, wasu kuma sun samu sau biyu ko uku.

“Sauran gidaje miliyan bakwai za su karɓi tallafin kafin ƙarshen shekara,” in ji Edun.

Ya ƙara da cewa ana biyan tallafin ne ta hanyar banki ko asusun wayoyi, ta hanyar amfani da lambar NIN na kowane wanda zai ci gajiyar.

Ministan, ya ce za a ci gaba da saka shirin a cikin kasafin kuɗin shekara-shekara domin ya ɗore.

Shugabar NASSCO, Hajiya Funmi Olotu, ta bayyana cewa dalilin biyan tallafin kashi-kashi, shi ne saboda umarnin Shugaba Bola Tinubu na haɗa tsarin da lambar NIN, domin tabbatar da gaskiya.

“Ba a raba kuɗi a hannu kai tsaye kamar da. Yanzu ana biyan kuɗi ne kai tsaye ta asusun banki. Wannan ne ya sa wasu gidajen suka riga suka karɓi sau ɗaya, biyu ko sau uku,” in ji ta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista
  • Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi
  • Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Jajantawa Al’ummar Gumi
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno