Fiye Da Falasdinawa 900,000 Ne Su Ka Yi Hijira A Cikin Gaza
Published: 24th, September 2025 GMT
HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 45 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin ‘yan sahayoniyar su ka kai.
Har ila yau an sami wasu Karin shahidan biyar a wuraren karbar agaji dake arewacin Rafaha.
A wani labarin mai alaka da hakan shugaban hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) Tedross Adhanom ya ce; Kai hare-haren da ake yi a kusa da asibitin Rantisy, dake Gaza, ya yi sanadiyyar tsayuwar aikin Asibiti, domin rashin tsaro.
Har ila yau ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa; Jinkirin shigar da makamashi zuwa yankin yana barazanar tsayar da aikin injinan da suke bayar da wuta a asibitin idanu,wanda yake yi wa mutane da dama aiki.
Ofishin hukuma a Gaza ya sanar da cewa, mutanen da sun kai 900,000 sun fice daga gidajensu amma kuma suna ci gaba da riko da ci gaba da zamansu a cikin kasarsu.
Bugu da kari, ‘yan mamayar suna ci gaba da tilastawa mutanen na Gaza ficewa daga gidajensu, zuwa yankunan kudancin Gaza, ta hanyar kai musu hare-hare.
Haka nan kuma da akwai wasu Karin mutanen 334,000 da aka fitarsa fita daga gidajensu a cikin kwanaki uku, da hakan ya sa yawansu ya kai 60,000.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya September 24, 2025 Larijani: Iran na kare tsaron kasa da azama September 24, 2025 Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Yin Watsi Da Inganta Sinadarin Uranium Ba September 24, 2025 Larijani: Iran Tana Nazarin Shawarwarin Turai Da Na Rasha Domin Kare Muradunta September 24, 2025 Araqchi; Iran Da Norway Sun Tattaunawa Batun kyakkyawar Alakar Da Ke Tsakaninsu September 24, 2025 Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran September 24, 2025 Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya September 24, 2025 Imam Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo September 23, 2025 Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jirgin Kasan Dakon Kaya Na Farko Daga Rasha Ya Iso Kasar Iran A Yau Asabar
A yau Asabar ne jirgin kasa na dakon kaya na farko daga Rasha ya iso tashar jiragen ruwa ta “Abrin” na Iran. Zuwan jigin kasan dai yana a karkashin bunkasa alakar kasuwanci ne a tsakanin Iran da Rasha.
Jirgin kasan yana dauke ne da hajar kasuwanci saboda kasuwannin Iran da kuma Iraki, yana kuma dauke da kwantena 62 masu girman kafa 40.
Shi dai wannan jirgin kasan ya taso ne daga wani yanki mai nisan kilo mita 900 daga Arewacin birnin Moscow, ya kuma ratsa ta kasashen Kazakhstan da Turkmenistan, sannan ya shigo Iran. Kwanaki 12 jirgin ya dauka akan hanya kafin a karshe ya yada zango a cikin Iran.
Gabanin tashin jirgin, sai an cimma yarjeniya da kasashen da zai ratsa ta cikinsu, da hukumominsu na tashoshin jiragen kasa, jami’an shiga da fitar kaya, da kuma cibiyoyin kasuwanci.
Zuwan jirigin kasan na Rasha zuwa Iran, yana a matsayin bude sabon shafi a harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu da kuma tsakanin Iran da kasashen Asiya ta tsakiya.
A baya a cikin watan Aprilu na wannan shekarar wani jirgin dakon kayar daga kasar China ya iso Iran,wanda shi ma yake a matsayin yunkurin bunkasa kasuwanci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail November 8, 2025 Araqchi: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin November 8, 2025 Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta November 8, 2025 Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci