Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-04@12:30:12 GMT

An Hori Musulmai Su Nuna Halin Dattako Da Tawali’u

Published: 20th, September 2025 GMT

An Hori Musulmai Su Nuna Halin Dattako Da Tawali’u

An shawarci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na tawali’u kamar yadda Annabi Muhammadu ya yi misali da su don yin rayuwa mai inganci.

 

Babban Limamin Masallacin Darul Khair Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ya bada nasihar ne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a garin Ilorin na jihar Kwara.

 

Ya ce yin rayuwar da za ta yi tasiri kai tsaye ga wasu za ta jawo lada mai kyau daga Allah.

 

A cewarsa ana sa ran musulmi za su gudanar da rayuwarsu daidai da koyarwar Alkur’ani da Hadisin Annabi Muhammad.

 

Imam Abdulrafiu-Onilaru ya bukaci al’ummar musulmi da su kasance masu kula da ‘yan uwansu da kuma taimaka wa mabukata.

 

Ya kuma yi kira gare su da su mutunta ji da ra’ayin jama’a domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a cikin al’umma

COV/ALI MUHAMMAD RABIU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara masallaci

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe ’yan bindiga 19 yayin daƙile wani hari a Kano

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan.

Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan motsinsu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse.

’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya

A sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar, sojojin sun gaggauta kai samame yankin bayan samun rahoto, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.

“A yayin arangamar, an hallaka ’yan bindiga 19, kuma an ƙwato babura da dama da wayoyin salula guda biyu daga hannunsu,” in ji Kyaftin Zubairu.

Sai dai ya tabbatar da cewa sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasu yayin fafatawar.

Kyaftin Zubairu ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da sintiri a yankin don kare al’ummomin da ke cikin haɗarin hare-haren masu satar shanu da sauran laifuka.

Rundunar ta kuma shawarci jama’a su kasance cikin shiri da lura, tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargin ba na halas ba ga jami’an tsaro mafi kusa.

A cewar kwamandan rundunar, Birgediya Janar Ahmed Tukur, Rundunar Sojin Najeriya na ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Kano, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

An bayyana wannan aikin a matsayin wani ɓangare na ci gaba da kare yankunan karkara domin bai wa mazauna ƙwarin gwiwa a wuraren da ake fama da hare-haren ’yan bindiga.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Musulmi : Falasdinawa ne kadai ke da hakkin jagorantar yankinsu
  • Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri
  • An kashe ’yan bindiga 19 yayin daƙile wani hari a Kano
  • Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza
  • Allah Ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa
  • Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu