Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki
Published: 1st, September 2025 GMT
Ƙungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, abin da ya ce “bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci.
Kungiyar ta roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya su shiga wajen tabbatar da kare haƙƙin ’yan Arewa da suke zaune a Legas.
Haka kuma ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sake duba matakin, ya samar da diyya da shirin sake mazauna kasuwar.
Gargaɗi kan zagin Sahabban Annabi Muhammad (SAW) An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a NejaSai dai Gwamnatin Jihar Legas ta kare kanta, tana mai cewa aikin na daga cikin shirin gyaran birni da ake aiwatarwa domin ƙara inganta tsaro da tsarin kasuwanni.
“Ba a yi wannan rushewar saboda ƙabila ko addini ba,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Tsara Birane ta jihar.
“Mun fara gyara wuraren da ba su dace ba don samar da sabuwar kasuwa mai tsari da aminci ga kowa.”
Gwamnatin ta ce tana nazarin matakan diyya da wurin da za a koma ga ’yan kasuwar da abin ya shafa, kodayake ba ta fitar da cikakken shiri ba tukuna.
Amma ABMPF ta yi watsi da bayanin gwamnatin, tana mai cewa ba a bi ƙa’ida wajen aiwatar da rusau ɗin ba, sannan ba a bai wa ’yan kasuwa isasshen lokaci ko inda za su koma ba.
“Abin takaici ne a kira al’ummar Arewa mazauna Alaba na tsawon shekara 80 da ’yan fiye da haka ’yan haya ko masu zama na wucin gadi da za a iya koran su duk lokacin da aka so,” in ji ƙungiyar.
Ta ƙara da cewa matakin yana nuna yunƙurin kawar da ’yan Arewa da ’yan yankin Gabas daga Legas, abin da zai iya haifar da rikice-rikice a wasu jihohin Arewa inda Yarbawa ke zaune cikin lumana.
Tasirin tattalin arzikiKasuwar Alaba Rago, wadda ta mamaye sama da hekta 10, wadda ta kasance cibiyar kasuwanci ga ’yan Arewa tun kafin samun ’yancin kai, ta tara dillalan dabbobi, hatsi da kayan gona da ake kawo su daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Masana tattalin arziki na gargaɗin cewa ruguza kasuwar zai iya shafar harkokin kasuwanci, kawo hauhawar farashi da rage harajin da jihar take samu daga irin waɗannan kasuwanni.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: diyya kasuwa Kasuwar Alaba Rago Yan Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.
Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp