Aminiya:
2025-09-24@09:55:55 GMT

Mun ci ribar Naira biliyan 601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT

Published: 24th, September 2025 GMT

Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025.

Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata.

Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata

Wannan na kunshe ne a cikin sakamakon binciken kudi kamfanin ya fitar, wanda ya ƙare ranar 30 ga Yuni, 2025.

Bankin ya kuma ce amma ribar kafin a cire haraji ce, idan aka cire kuma za ta koma biliyan 449.01, idan aka kwatanta da biliyan 905.57 a daidai wannan lokaci na shekarar 2024.

Duk da raguwar kudaden shiga, hukumar gudanarwar bankin ta amince da biyan ribar Naira 1.00 ga duk masi hannun jari a cikinsa, kamar yadda aka yi a rabin farko na 2024.

Za a biya wannan ribar ce ga masu hannun jari da sunayensu ke cikin rajistar mambobi a ranar 7 ga Oktoba, 2025.

Sai dai ribar kamfanin ta ragu da kashi 43.5 cikin 100 a zangon farko na 2025 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, sakamakon faduwar darajar daga kadarorin kudi kamar takardun bashi da takardun baitul-mali.

Ribar da ba a tabbatar ba daga darajar kadarorin kudi na bankin, wanda yawancin kadarorinsa ke cikin takardun kudi fiye da rance ga abokan ciniki, ta fadi zuwa Naira biliyan 1.5 daga Naira biliyan 331.6.

Wannan ya haifar da raguwar sauran kudaden shiga, wanda shi ne ginshiƙin kudaden shiga na kamfanin a bara, da kashi 91.8 cikin 100.

Jimillar kudaden shiga na bankin ya fadi zuwa Naira biliyan 523.2 daga Naira biliyan 680.5 a cikin wannan lokaci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Naira biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Kefas Ya Bamu Damar Ƙwatar Mulkin Taraba A 2027 – APC

Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta yi yi kakkausar suka ga mulkin Gwamna Agbu Kefas, inda ta ce bayan shekaru biyu a ofis ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Jam’iyyar ta ce rashin tasirin gwamnatin PDP zai sauƙaƙa wa APC kwace mulki a shekarar 2027 a jihar.

Da yake magana a Jalingo, Sakataren APC na jihar, Fidelis Francis, ya zargi Gwamna Kefas da rashin ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa, ciki har da barin hanyar zuwa ƙaramar hukumar gwamnan a lalace bayan gadoji sun karye. Ya bayyana mulkin nasa a matsayin “wanda bai shirya ba kuma ba shi da wani tsari.”

Francis ya ƙara da cewa PDP tun daga 1999 ba ta da abin da zata nuna wa jama’a a matsayin na ci gaba, yana mai jaddada cewa gwamnatin Kefas kawai “fentin gine-ginen da aka yi tun da yake yi, tana iƙirarin ayyukanta ne.” Ya ce: “Gwamnan ya taimaka mana da kashi 80 cikin dari. Ya yi aikin da zai sauƙaƙa wa jam’iyyar adawa ta karɓo mulki saboda ba shi da komai da zai nuna.”

Ya buƙaci mambobin APC da su kwantar da hankali tare da haɗa kai domin shiryawa zaɓen 2027, yana mai tabbatar musu cewa jam’iyyar ta koyi darasi daga kura-kuran baya. “Mutanen Taraba ba su da hujjar sake zabar Gwamna Kefas,” in ji shi, yana mai cewa APC ta riga ta fara dabarun da za su kayar da PDP a zaɓen mai zuwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutum 4,383, Sun Ceto 1,138 Daga Hannun Mahara Cikin Wata 3
  • Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
  • UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya
  • Babban Bankin Nijeriya Ya Rage Kuɗin Ruwan Da Bankuna Ke Caja
  • CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100
  • DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
  • Gwamna Kefas Ya Bamu Damar Ƙwatar Mulkin Taraba A 2027 – APC
  • Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI
  • 2027: ‘Ku Yi Zaɓe Bisa Ga Ra’ayin Kanku, Ba Lura Da Ƙabila Ko Yanki Ba’, – Atiku Ga ‘Yan Nijeriya