A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin.

An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye.

(Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai

Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 ​​a cikin  masai.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a.

Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800

Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai.

“Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Daraktan, Sani Anas ta samu kiran gaggawa daga Usman Adamu da misalin ƙarfe 9:27 na safiyar ranar Alhamis, 6 ga watan Nuwamba, 2025, inda ya bayar da rahoton ibtila’in da wata mata ta faɗa cikin ramin masai a ƙauyen Sarai da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu,” a cikin sanarwar.

“Jami’anmu na sashen agajin gaggawa daga hedikwatar hukumar ta isa wurin, inda ta gano wata mata mai suna Habiba Ado mai shekara 96, wanda ’yan uwanta suka ce tana fama da taɓin hankali,” in ji shi.

Abdullahi ya bayyana cewa, ‘yan uwanta ​​sun shafe kwanaki huɗu suna nemanta kafin a gano gawarta a cikin masai ranar Alhamis.

“Sun kuma yi kira ga mai gidan da ya rufe ramin masan don hana afkuwar irin haka nan gaba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami’an ceto sun gano  matar daga cikin ramin, amma an tabbatar da mutuwar ta.

Tuni dai aka miƙa gawarta ga Hakimin Unguwa, Alhaji Musa Muhammad domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil
  • An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai
  • Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe
  • Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
  • Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan
  • Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
  • Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya
  • Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE