NEF za ta ƙaddamar da taron zuba jari don bunƙasa Arewa
Published: 22nd, September 2025 GMT
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce a karon farko za ta shirya taron zuba jari da samar da masana’antu na Arewacin Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba a Abuja.
Taron wanda aka shirya tare da hadin gwiwar jihohin arewa 19 da kuma kamfanin raya yankin – NNDC, na da nufin mayar da yankin a matsayin wata cibiya ta samun bunkasar tattalin arziki da habaka masana’antu.
Da yake magana a taron manema labarai da aka gudanar ranar Litinin a Abuja, kakakin kungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana taron a matsayin “kira domin zaburar da tattalin arziki da kuma tsare-tsare na cika alkawarin Arewacin Najeriya.”
Ya ce an tsara taron ne a cikin watanni 18 da suka gabata domin kaddamar da wani shiri na kishin kasa wanda zai karfafa ayyukan ci gaba da bude sabbin kafofin damammanki ga yankin, Najeriya da abokan huldar kasa da kasa.
“Wannan taron ba na siyasa ba ne, yana mai da hankali kan tattalin arziki, kan damammaki, da kuma samar da wadata. Yana da zimmar nuna karfin Arewacin Najeriya da kuma gabatar da hangen nesa na ci gaba, kirkire-kirkire, da haɗin gwiwa. Daga yau, za mu bude sabon babi,” in ji Jiddere.
Da yake yin la’akari da irin gudunmawar da yankin ya bayar a tarihi, ya tuna cewa a shekarun 1960 zuwa farkon 1980, Arewacin Nijeriya ya ba da karfin tattalin arzikin kasa ta hanyar noma, masana’antu, da kasuwanci. “Dalarmu na gyada ya kai sararin sama; auduga, fatu, dabbobi, da ma’adanai masu ƙarfi suna tallafawa masana’antu,” in ji shi.
Duk da haka, ya ce rashin tsaro da rashin zuba jari sun rage ci gaban yankin, wanda ya haifar da rikice-rikice na albarkatu masu yawa da kuma abubuwan da ba a san su ba, “Wannan taron yana manufa juya akalar rikicin zuwa ga damammaki da kuma tabbatar da cewa Arewacin Najeriya ya samu kwarin gwiwa zuwa wani sabon zamani na ci gaba,” in ji shi.
Jiddere ya zayyana ginshiƙai masu mahimmanci guda biyar da yankin yake tutiya da su kamar albarkar ƙasa da noma, manyan ma’adanai, albarkatun ɗan adam, ababen more rayuwa, da masana’antu, waɗanda ke samun tallafi kamar ilimi, kiwon lafiya, gidaje, da fasaha.
Ya nanata cewa Arewacin Najeriya “yana da alaƙa da kasa-wata babbar hanyar shiga Nijar, Chadi, Kamaru, Benin, Mali, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.”
Ya ƙalubalanci masu ruwa da tsaki da su yi nazari a kan abubuwan da ba za a iya amfani da su a yankin ba, yana mai tambaya, “Ta yaya yankin da ya samar da shugabanni da masu ƙirkire-ƙirkire a duniya, ’yan ƙato da gora irin su Alhaji Aliko Dangote da Amina Mohammed, har yanzu bai nuna cikakken ƙarfin tattalin arzikinsa ba?
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa Dattawan Arewa Arewacin Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA