An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan
Published: 20th, September 2025 GMT
A yau Juma’a ne aka rufe taron dandalin tattauna batun tsaro na Xiangshan karo na 12 a birnin Beijing, bayan mahalartansa sun zurfafa tattaunawa karkashin jigon “Mara baya ga odar kasa da kasa da ingiza ci gaba cikin lumana.”
An bude taron ne a ranar Laraba, ya kuma hallara sama da wakilai 1,800, ciki har da jami’an gwamnatoci, da kwararru, da masana da wasu masu sanya ido daga kasashe, yankuna da hukumomin kasa da kasa sama da 100.                
      
				
Mahalarta taron, sun zanta karkashin jigo daban daban, ciki har da “Gina tsarin adalci da daidaito na shugabancin harkokin tsaron kasa da kasa,” da jigon “Amincewa da juna bisa matsayin koli da hadin gwiwar tsaro a yankin Asiya da Fasifik”. Sai jigon “Odar kasa da kasa da tsaron duniya da samar da daidaito,” da kuma “Gina zaman lafiya na shiyyoyi karkashin tsarin tattaunawa da gudanar da shawarwari.”
Taron ya kuma bayar da damar tattaunawa tsakanin manyan kwararru, da dakarun sojoji da malamai, kana an gudanar da wasu tarukan karawa juna sani na sirri, wanda hakan ya ingiza musayar koyi da juna, da fadada kafofin tattaunawa tsakanin Sin da mahalarta tsaron na sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa na ƙasa.
Shugaban sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya shigo daga jihar Ribas ne musamman domin amfani da taron siyasar da aka shirya wajen yin sata.
Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a NajeriyaYa ce jami’ansu sun kama shi ne bayan sun lura da motsinsa da ya sa suka zarge shi. Bayan bincike, sai suka gano wayoyi 17, kudi N91,000, da kuma katunan ATM da dama a cikin jaka da yake dauke da ita.
Alagba ya kara da cewa, Francis ya shaida musu cewa yana aiki tare da wasu abokan laifi da suka tsere yayin kamun.
Ya kuma bayyana cewa kafin a kama shi, sun riga sun kwashe sama da N400,000, sannan daya daga cikin wadanda suka gudu yana da karin wayoyi da sauran kayayyakin da suka sace.
Shugaban sa-kai din ya gargadi masu aikata laifuka da su guji shiga Bayelsa, yana mai cewa jami’ansa sun samu horo na musamman kan tattara bayanan sirri, lura da halayen jama’a da kuma tsaron taruka.