Araghchi ya Tattauna da takwarorinsa na kasashen Girka da Slovenia da Saliyo
Published: 6th, September 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran, Seyyed Abbas Araghchi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaroribnsa na kasashen Girka, Slovenia da Saliyo a wannan Juma’a kan batutuwan da suka shafi kasashen.
Mista Abbas ya gana ne Georgios Gerapetritis, ministan harkokin wajen Girka, Tanja Fajon, ministan harkokin wajen Slovenia, da Alhaji Musa Timothy Kabba, ministan harkokin wajen Saliyo.
Dukkan kasashen uku a halin yanzu mambobi ne a kwamitin sulhu na MDD.
Tattaunawar ta ta’allaka ne kan dangantakar da ke tsakanin Iran da kasashen, da kuma ci gaban yanki da na kasa da kasa, musamman dangane da matakin da kasashen Turai uku (Birtaniya, Faransa, da Jamus) suka yi a kwamitin sulhu.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kakkausar suka kan matakin da kasashen Turai uku suka dauka na farfado da kudurorin kwamitin sulhun da tuni aka soke, wadanda a cewarsa ba su dace ba, kuma sun sabawa doka.
Mr. Araghchi ya jaddada bukatar samar da hanyoyin diflomasiyya don warware takaddamar da ake fuskanta dangane da shirin nukiliyar Iran cikin lumana.
A nasu bangaren, ministocin harkokin wajen kasashen Girka, Slovenia, da Saliyo, sun jaddada goyon bayansu ga warware takaddamar ta hanyar diplomasiyya, tare da jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da kuma kaucewa tabarbarewar tsaro.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : Adadin Wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila cikin sa’o’I 24 ya karu September 6, 2025 Kungiyoyin gwagwarmaya sun fusata da barazanar Isra’ila na bude “kofofin jahannama” a Gaza September 6, 2025 Iran ta aike da kayayyakin jin kai tan 100 zuwa Afghanistan September 6, 2025 Ammar Hakeem ya gana da larijani a nan birnin Tehran . September 6, 2025 HKI Ta Kashe Falasdinawa 50 A Harin Da Takai A Yankin Gaza September 6, 2025 An yi Kira Ga El-rufai Da Ya yi Hattara Da Kalamansa September 6, 2025 An Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Shirin Amurka Na Kwace makaman Hizbullah. September 6, 2025 Manyan Jami’an Kungiyar Hamas sun Gana Da Minister Harkokin Wajen Iran September 6, 2025 Afirka za ta iya samun tagomashi wajen habaka tattalin arzikin dijital – IFC September 6, 2025 Araqchi: Kasashen Turai Suna Nuna Son Kai A Kan Batun Hana Kera Makamin Nukiliya September 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI
Shugabgan kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da fira ministan kasar Iraqi Muahmad Shi’a Sudani a taron Doha na kasashen musulmi ya bayyana cewa; Wajibi ne kasashen musulmi su hada kai idan har suna son kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa.
Bugu da kari, shugaban kasar ta Iran ya kuma tattaunwa wasu hanyoyin da ya kamata a yi aiki da su, matukar ana son kawo karshen ta’addancin ‘yan sahayoniya.
Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce, laifukan da HKI take tafkawa akan fararen hula a Gaza, da kashe yara da mata ta hanyar yunwa, wani lamari ne da hankali bai iya daukarsa, kuma idan musulmi su ka hada hannu da karfe wuri daya za su kawo karshensa.
A nashi gefen Fira ministan kasar Iraki ya bayyana abinda HKI take yi da cewa, isgili ne da dokokin kasa da kasa,don haka nauyi ne da ya doru a wuyan kasashen musulmi da su yi aiki domin ganin dukar matakan da suka dace.
Haka nan kuma ya ce, taron na birnin Doha dama ce ta daukar irin wadannan matakan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci