He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
Published: 23rd, September 2025 GMT
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing.
He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya, tare da samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don tabbatar da daidaiton dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a mataki na gaba.
Ana sa ran Amurka za ta sa kaimi wajen yin magana da kasar Sin bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da samun nasara ga ko wane bangare, da kara amincewa da juna, da kawar da shakku, da sa kaimi ga habaka dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ana fatan mambobin majalisar wakilan Amurka za su himmatu wajen samar da hanyoyin zantawa, da inganta tattaunawa da mu’amala, da kuma taka rawar gani wajen ci gaban kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Mallaki Kusan Tashoshin Fasahar 5G Miliyan 4.65
Yawan tashoshin fasahar sadarwa ta 5G a kasar Sin ya kai kusan miliyan 4.65 a karshen watan Agusta, kamar yadda alkaluman mahukunta suka nuna a yau Talata.
A cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, adadin ya kai kashi 36.3 na adadin tashoshin sadarwar wayar hannu a fadin kasar baki daya.
A halin yanzu, ana samun karuwar masu wayar salula a kasar Sin da ke rungumar amfani da fasahohin sadarwa na 5G.
Alkaluman da aka fitar zuwa karshen watan Agusta sun nuna cewa, yawan masu amfani da wayar salula na manyan kamfanonin sadarwa uku da kuma kamfanin China Broadnet ya kai kimanin biliyan 1.82. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp