DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
Published: 23rd, September 2025 GMT
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi.
An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin cikin ƙwarewa da mutuntawa.
A ranar 1 ga Satumba, 2025 ne aka kai wa ayarin motocin da ke rakiyar Malami hari a Birnin Kebbi, bayan ya dawo daga gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Babban Limamin Masallacin Dakta Bello Haliru Jumu’a.
Shaidu sun bayyana cewa an lalata motocin rakiyarsa kusan guda 10, sannan da dama daga cikin magoya bayansa sun jikkata.
Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC ’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a KebbiMalami ya yi zargin cewa harin yana da nasaba da siyasa, duk da cewa jam’iyya mai mulkin jihar — APC, ta nesanta kanta daga lamarin.
Daga bisani Malami ya shigar da ƙorafi zuwa ga hukumomin tsaro, ciki har da ’yan sanda da DSS.
A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Litinin, Malami ya ce an gudanar da binciken cikin gaskiya da ƙwarewa, tare da nuna masa mutuntawa.
“Na tabbatar cewa DSS ta gayyace ni domin bayar da gudunmawa wajen binciken harin da aka kai mini da ’yan rakiyata a Kebbi a ranar 1 ga Satumba, 2025.
“Ƙorafin ya samo asali ne daga manyan ’yan adawa a jihar. Ina yaba wa hukumar DSS bisa yadda suka gudanar da binciken cikin gaskiya da mutunci.
“An yi min tambayoyi cikin mutuntawa, kuma zan ci gaba da bayar da haɗin kai don tabbatar da kammala binciken yadda ya kamata,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka
Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa kamfanonin cikin gida za su iya gabatar da bukata da neman yin ciniki da kamfanonin Amurka da aka ambata a sama da zarar an amince da bukatunsu. (Amina/Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA