Ko Me Ya Sa Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ke Kara Janyo Hankalin Al’ummun Duniya?
Published: 20th, September 2025 GMT
A shekarar 2025 a gundumar Qiemo dake jihar Xinjiang ta kasar Sin, wasu sabbin sassan dausayi da ake iya nomawa sun bayyana a cikin makeken yankin hamada. A ’yan shekarun nan, an gyara yankin rairayi zuwa gonaki, wadanda fadinsu ya zarce murabba’in kilomita 40 a gundumar Qiemo. A cikin sama da shekaru 10, an yi kokarin raya wasu sassan dausayi da ake iya nomawa a cikin yankin hamada dake jihar Xinjiang, inda fadin gonakin da ake noman hatsi ya karu zuwa murabba’in kilomita dubu 8 ko fiye, al’amarin da ya sa Xinjiang ta zama jihar da ta fi samun karuwar hatsi da ake nomawa a duk fadin kasar Sin.
A bana ne ake cika shekaru 70 da kafa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ta kasar Sin, inda ake yawan ganin irin wannan labari mai dadi a duk fadin jihar, kuma Xinjiang na kara janyo hankalin jama’a daga sassan kasa da kasa.
A shekara ta 2024, adadin baki ’yan kasashen waje da suka shiga jihar don yawon bude ido ya wuce miliyan 5, adadin da ya karu da kaso 46 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2023. Wadannan baki ’yan kasashen waje sun zama masu gani da ido game da ci gaban jihar Xinjiang. Daya daga cikin sanannun mutane a shafukan sada zumunta na intanet, Ba’amurke Danny Haiphong, ya ce “A wasu lokuta, abubuwan da muke gani a kafafen yada labaran yammacin duniya, ba sa bayyana abubuwa masu kyau. Amma muna jin dadin rayuwa a jihar Xinjiang dake da yanayi mai annashuwa.”
A halin yanzu, akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali, da wadata da kyan muhalli a jihar Xinjiang, inda jama’a ke jin dadin rayuwa da aiki a wurin, al’amarin da ya shaida nasarorin muhimman manufofin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ke aiwatarwa a jihar a sabon zamani. Kana, a karkashin wadannan manufofi, an samu manyan sauye-sauye, gami da dimbin nasarorin da ba a taba ganin irinsu ba a tarihin jihar, inda aka shiga wani muhimmin lokaci na samun babban ci gaba, da gagarumin sauyi, kana jama’a suna kara samun moriya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a jihar Xinjiang ta kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro.
Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu.
Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro?
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan