Ɓarkewar cutar Ebola ta kashe mutum 15 a Congo
Published: 5th, September 2025 GMT
Mahukuntan lafiya sun tabbatar da sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuryar Dimokraɗiyyar Congo wadda zuwa ƙarshen watan Agustan da ya gabata ta yi ajalin mutum 15 a lardin Kasai da ke tsakiyar ƙasar.
Ministan Lafiya, Samuel Roger Kamba, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Kinshasa, babban birnin ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa an samu mutum 28 da ake zargin sun kamu da cutar a lardin Kasai, inda a karon farko a ranar 20 ga watan Agusta aka gano ta a jikin wata mata mai juna biyu mai shekara 34 bayan kwantar da ita a asibiti.
“Wannan shi ne karo na 16 da aka samu ɓarkewar Ebola a ƙasarmu,” in ji Ministan Kamba.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce adadin masu cutar na iya ƙaruwa, inda ta riga ta tura ƙwararrunta tare da tawagar ƙungiyar agajin DRC zuwa lardin Kasai domin ba da gudummawar daƙile yaɗuwar cutar.
A cewar Darektan WHO na Afirka, Mohamed Janabi, akwai magungunan da aka tanada da allurai 2,000 na rigakafin cutar Ebola, waɗanda za a tura daga Kinshasa zuwa Kasai nan ba da jimawa ba.
Cutar Ebola, wacce aka fara gano ta a shekarar 1976 daga ɓerayen daji, cuta ce mai haɗari da ke yaɗuwa ta hanyar hulɗa da jini ko ruwa a jikin mai cutar.
Ɓarkewar cutar mafi muni a tarihin DRC ta faru ne tsakanin 2018 zuwa 2020, inda aka rasa rayukan fiye da mutum 2,300.
A yanzu haka, hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa irin nau’in Zaire na Ebola ne ya sake ɓulla, wanda ake da rigakafi a kansa.
“Abin farin ciki shi ne akwai rigakafin nau’in Zaire, amma kafin a fara yi wa jama’a allurar, sai an kammala shirin tsara dabarun isar da ita,” in ji Ministan Lafiya Kamba.
Wannan ne karo na 16 da ake samun ɓarkewar cutar a ƙasar tun bayan da aka fara ganota kusan shekara 40 da suka gabata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo cutar Ebola
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp