AU: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Bunkasa Noma Na Da Matukar Muhimmanci
Published: 2nd, September 2025 GMT
Mukaddashin daraktan ofishin bunkasa tattalin arziki, hada kai da raya cinikayya a hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, mista Patrick Ndzana Olomo, ya ce nahiyar Afirka da Sin na da makoma mai haske a fannin raya hadin gwiwa, don bunkasa harkokin noma da shawo kan matsalar kamfar abinci a Afirka.
Olomo, wanda ya yi tsokacin a ranar Juma’a yayin da ya ziyarci cibiyar gwajin fasahohin noma, inda kwararrun kasar Sin ke baje kolin fasahohin zamani na inganta noma dake birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha, ya ce kasashen Afirka da Sin na aiki tare wajen samar da gamammen tsarin bunkasa noma, wanda zai ingiza matsayin nahiyar Afirka zuwa ga cimma nasarar samar da isasshen hatsi da wadatuwar abinci.
Masaniyar aikin gona ta hukumar gudanarwar kungiyar AU Patience Mhuriro-Mashapa ita ma ta yabawa irin ci gaban da alakar sassan biyu ta samu zuwa mataki mafi muhimmanci a tarihi, ta kuma jinjinawa kwazon kasar Sin na aiki tare da bangaren Afirka, a fannin bunkasa fasahohin zamani na noma, inda ta ce kwararrun kasar Sin sun jima suka aiki tare da takwarorinsu na Afirka wajen gina sabbin tsare-tsaren raya noma, da gabatar da sabbin nau’o’in irin shuka, da inganta dabarun samar da yabanya mai yalwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp