‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
Published: 23rd, September 2025 GMT
‘Yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Pankshin Kudu, Laven Denty, a gidansa da ke unguwar Dong na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A makon da ya gabata ma, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin unguwar Dong, inda suka yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), da kuma ɗalibin Jami’ar Jos.
Masu garkuwar da mutanen sun shiga gidan iyalan Solomon Dansura, da misalin ƙarfe 10 na dare inda suka tafi da baƙinsa guda biyu a lokacin.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin jihar ko kuma tabbaci daga rundunar ‘yansandan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ɗan Majalisa Garkuwa Yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25.
“An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.”
‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka yi suna kamar masu garkuwa da mutane.
“An bar wayar salula ta wanda ya bace a dakinsa. Jami’an bincike suka bi layin kira daga lambar 0906193291, inda aka gano tana hannun wani fursuna da ake tsare da shi a cibiyar gyaran hali ta Igbara, Abeokuta, saboda wani laifin garkuwa da mutane.
“Wanda ake zargin ya ce sun ga lambar wayar a kafafen sada zumunta, suka yi amfani da ita don cutar da mahaifin wanda ya bace, Mista Anyanwu Simon, mai shekara 56. An biya kudin Naira 100,000 zuwa asusun Opay mai lamba 7042793493 na wata Atinuke Oluwalose, abokiyar hadin bakin fursunan da ke gidan yarin Abeokuta.”
“Daga bayanan da jami’an bincike suka gano, akwai wasu abubuwan damuwa da ka iya kasancewa silar abin da ya faru. An gano wasu kalaman da wanda ya bace ya yi dangane da wasu sabbin dabi’u da sha’awowi da ba su dace da akidar addininsa ba,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kammala da cewa ana ci gaba da daukar matakan bincike “domin tabbatar da sakamakon da jami’an bincike suka tattara, kasancewar binciken ya fito da abubuwa masu ban mamaki. Ba a samu wata alamar garkuwa da mutane a wannan lamari ba. Ana ci gaba da aiki domin samun cikakken bincike.”
PUNCH Metro ta ruwaito a watan Oktoba 2024 cewa an kama mutum hudu kan bacewar wani dan NYSC mai suna Yahya Faruk, wanda yake hidima a Ikuru, cikin Karamar Hukumar Andoni ta jihar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA