Iran za ta katse hulda da IAEA idan aka maida mata takunkuman MDD
Published: 20th, September 2025 GMT
Iran ta yi gargadin cewa za ta kawo karshen duk wata yarjejeniyarta da hukuar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, muddin ake sake dawo mata takunkuman MDD.
Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya ce Tehran za ta dakatar da hadin gwiwar da take yi da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar dage takunkumin da aka kakabawa Tehran na dindindin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Asabar, babban jami’in tsaron kasar Iran ya yi Allah wadai da matakin “marasa hankali” da Birtaniya, Faransa, da Jamus –wanda aka fi sani da E3– game da shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin lumana
Mataimakin ministan shari’a da harkokin kasa da kasa na kasar Iran Kazem Gharibabadi ne ya bayyana hakan, inda ya ce yarjejeniyar da aka cimma a baya-bayan nan tsakanin Tehran da hukumar ta IAEA a birnin Alkahira za ta kawo karshe idan Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata takunkuman, da ake kira “snapback” a turance.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da matakin bayan da ya kasa samun kuri’un da suka dace.
“kasashen Sin da Rasha sun bayyana cewa, matakin da wadannan kasashe uku suka dauka ya sabawa doka.”
A ranar 9 ga watan Satumba ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da darakta janar na hukumar IAEA Rafael Grossi suka cimma matsaya kan tsare-tsare masu amfani na maido da hadin gwiwa bayan wata ganawa da suka yi a birnin Alkahira na kasar Masar.
Wannan mataki dai ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin kasar Iran baki daya ta amince da wata doka da ta bukaci Iran ta dakatar da duk wani hadin gwiwa da hukumar ta IAEA, biyo bayan harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar guda uku, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta NPT.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Venezuela ta bukaci MDD ta binciki harin da Amurka ta kai a yankin Caribbean September 20, 2025 Spain za ta hada kai da kotun ICC domin gudanar da bincike kan laifukan da Isra’ila ta aikata a Gaza September 20, 2025 Falasdinawa 47 sun yi shahada a Hare-haren Isra’ila September 20, 2025 Sudan: Rundunar Daukin Gaggawa ( R.S.F ) Ta Kashe Mutane 75 A Wani Hari Da Ta Kai Wa Masallaci A Garin Al-Fasha September 20, 2025 Pakistan: Makaman Nukiliyarmu Suna Cikin Yarjejeniyar Tsaro Da Mu Ka Kulla Da Saudiyya September 20, 2025 Adadin Falasdinawa Da HKI Ta Kashe Da Jikkatawa Sun Haura 230,000 September 20, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Kira Yi Saudiyya Da Ta Bude Sabon Shafi Da Gwagwarmaya September 20, 2025 Arqchi: Iran Ba Ta Amince Da Duk Wani Matakin Matsin Lamba Da Rashin Adalci Ba September 20, 2025 Jakadan Iran A MDDuniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna September 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada ‘Yancin Kasar Na Mayar Da Martani Kan Sabawa Doka September 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce
Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususluni na bayyana yaƙin kwanaki 12 kan Iran ya tabbatar da cewa ba za a taɓa amincewa da Amurka ba
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ya tabbatar da cewa: Yakin kwanaki 12 da aka yi da Iran ya nuna rashin amana ga masu yanke shawara na Amurka, kuma al’ummar Iran sun san halin da ake ciki kuma sun haɗu wuri ɗaya, inda suka samar da garkuwar da ba za a iya ratsawa ba.
Birgediya Janar Ali Mohammad Na’ini, kakakin Dakarun kare juyin juya halin Musulunci {IRGC}, ya yi jawabi ga mahalarta taron gangamin Ranar Yaƙi da Girman Kai na Duniya a Karaj, yana mai nuna godiyarsa ga kasancewar mutane masu aminci da juyin juya halin Mususlunci na Lardin Alborz a taron gangamin ƙasa a ranar 13 ga Aban (13 ga Nuwamba). Ya bayyana cewa wannan gangamin shi ne na farko tun bayan da aka kakaba wa Iran yaƙin kwanaki 12, ya sake nuna jajircewar jama’a ga taken juyin juya halin, ruhinsu na kalubalantar girman kai, da kuma haɗin kan al’ummar Iran ga kafofin watsa labarai na duniya.
A cikin jawabinsa, yayin bikin tunawa da ranar shahadar shugabar matan duniya Sayyidah Fatima Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta), yana mai jaddada cewa ranar 13 ga Nuwamba ba wai kawai tunawa da wani abin da ya faru a baya ba ne ko sake duba wani abu mai sauƙi na tarihi, kuma sanya wannan rana a matsayin “Ranar Ƙasa ta Yaƙi da Girman Kai na Duniya” ba aiki ne kawai na alama ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Admiral Sayyari Ya Ce: Isra’ila Ba Ta Kai Matsayin Da Zata Yaki Iran Ba November 4, 2025 Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Ya Jaddada Gagarumin Tsaron Kasa Da Gwagwarmaya Ta Baiwa Lebanon November 4, 2025 Mataimakin Tsohon Shugaban Kasar Amurka Dick Cheney Ya Mutu A Yau Talata November 4, 2025 Ana Tattara Gawawwakin Mutanen Da Mayakan Rapid Support Forces Suka Kashe A Arewacin Kordofan Na Sudan November 4, 2025 Iran : Jagora ya gindaya wasu sharudda kafin yin duk wata hulda da Amurka November 4, 2025 Kasashen Musulmi : Falasdinawa ne kadai ke da hakkin jagorantar yankinsu November 4, 2025 Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci November 4, 2025 Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci