Aminiya:
2025-11-08@15:38:04 GMT

Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC

Published: 23rd, September 2025 GMT

Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da sojoji ke mulki sun sanar cewa sun fice daga Kotun Duniya ta Hukunta Manyan Laifuka (ICC).

A sanarwar da suka fitar ranar Litinin sun bayyana ICC a matsayin “kayan aikin mulkin mallaka na zamani.”

Ƙasashen ukun, waɗanda aka yi juyin mulki a cikinsu tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023, sun kafa ƙawance mai suna Kungiyar Kasashen Sahel (AES) domin haɗa kai da nisantar da kansu daga ƙasashen Yamma, musamman tsohuwar mai mulkinsu, Faransa.

A cikin sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ƙasashen sun ce kotun da ke birnin Hague “kayan aikin danniya ce a hannun masu mulkin mallaka.”

’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance

Sun ƙara da cewa, “ICC ta kasa tabbatar da shari’o’in manyan laifuka da suka haɗa da laifukan yaƙi, kisan gilla ga bil’adama, kisan ƙare dangi da kuma laifukan cin zarafin ƙasa.”

Sun ce suna shirin kafa “hanyoyin cikin gida domin tabbatar da zaman lafiya da adalci.”

Doka ta tanadar cewa ficewar kowace ƙasa daga ICC zai fara aiki ne shekara guda bayan an miƙa sanarwar ficewar ga Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tun bayan kafa AES, Burkina Faso da Mali da Nijar sun ƙara kusanci da ƙasashe irin su Rasha, wadda Shugabanta Vladimir Putin ke fuskantar sammacin kame daga ICC tun watan Maris 2023 kan yaƙin da ake yi a Ukraine.

Sai dai ƙasashen ukun na fama da hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyin masu alaƙa da Al-Qa’ida da Daesh, yayin da ake kuma zargin sojojinsu da aikata laifuka kan fararen hula.

Kotun ICC dai an kafa ta ne a 2002 domin gurfanar da waɗanda suka aikata manyan laifuka — musamman na yaƙi — a inda gwamnati ba ta da ikon ko kuma ba ta da niyyar ɗaukar mataki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Nijar

এছাড়াও পড়ুন:

Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah

Bishop Matthew Kukah, na Cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato, ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo wa Najeriya ya farkar da shugabannin ƙasar nan. 

Trump, ya zargi Najeriya da cin zarafin Kiristoci tare da barazanar janye tallafin Amurka ko kuma ɗaukar matakin soja domin “ceto Kiristoci” a ƙasar.

Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu

Sai dai Shugaba Bola Tinubu, ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cikakkiyar dimokuraɗiyya mai mutunta ’yancin yin addini.

Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 60 na ɗan jarida Reuben Abati a Jihar Legas, Kukah, ya ce kalaman Trump na nuna akwai matsaloli a Najeriya.

“Muna ganin Trump a matsayin  matsala. Amma Trump alama ce ta rashin lafiyar da ke cikin ƙasarmu,” in ji Kukah.

“Ko Trump ne ko wani daban ya tunzuramu, lokaci ya yi da Najeriya za ta farka.”

Ya kuma soki rashin wuraren yawon buɗe ido da abubuwan tarihi da za su nuna ainihin abubuwan da Najeriya ta mallaka.

“Idan wani ya zo Najeriya yau, ina za ka kai shi? Dole mu sake gina ƙasarmu da kuma bayyana tarinhinmu a matsayin ’yan ƙasa,” in ji shi.

Kukah ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi tunani mai zurfi tare da ɗaukar nauyin gina ƙasa mai haɗin kai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah
  • NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura
  • Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza
  • Kwamitin Tsaron Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza
  • Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax
  • An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bi Sa Tuhumar  Fitar Da Bayanai Na Hukuma
  • DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa
  • Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi